News
Gwamnatin Jihar Kano Ta Haramta Dukkan Fina-finan Dake Nuna Fadan Daba Da Harkar Daudu A Fadin Jahar

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Biyo bayan korafe-korafen da al’umma keyi a kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar Daudu a jahar Kano. Shugaban Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta jahar Kano Abba El-mustapha ya bada umarnin dakatarwa tare da hana dukkan fina-finan dake nuna fadan daba da harkar daudu a fadin jahar Kano.
Abba El-mustapha na bada wannan umarni ne a yau jim kadan bayan wata ganawa da yayi da manyan ma’aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano tare da wasu daga cikin wakilan yan masana’antar shirya fina-finan ta kannywood wanda suka hada da kungiyoyin MOPPAN, AREWA FILMS MAKERS DIRECTORS da kuma PRODUCERS.
Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ma’aikatar tace Fina-Finai Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar
Hukumar JAMB Ta Sake Tsawaita Lokacin Rajistar Neman Gurbin Karatu Na DE
Haka zalika Abba ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar dakatarwa ko hana duk wani film da take ganin yaci karo da tarbiya tare da al’adar al’ummar dake jahar, a saboda haka tuni lokaci ya shige da za’a saka ido irin wannan gurbatattun fina-finai su cigaba da yaduwa a cikin al’umma.
