News
Hukumar Kashe Gobara Ta Ceci Rayuka 12 Tare Da Ceto Dukiyar Naira Miliyan 130 A Cikin Wata Daya A Kano
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta bayar da rahoton watan Maris, inda ta ceto mutane 12 tare da ceto Dukiyar Naira miliyan 130 daga jimillar gobara 78.
Alhaji Saminu Abdullahi, Jami’in Hulda da Jama’a na Hukumar, ne yabai yana hakan a zantawar sa da Kamfanin Dillancin Labarai Na Kasa NAN ranar Laraba.
Rundunar sojin Najeriya ta zargi sarakunan Delta da hannun a kisan sojojinta 17
Abdullahi ya bayyana cewa duk da cewa jami’an kashe gobara sun yi nasarar shawo kan mafi yawan gobara, amma Mutane 10 ne suka rasa rayukansu a wata gobara da ta tashi a watan Maris, kuma an yi asarar dukiya ta Naira miliyan 71.
Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta mayar da martani ba kawai ga tashin gobara ba, har ma da kiraye-kirayen ceto guda 27 da kuma kararrawar karya 11 daga mazauna yankin a tsawon wannan wata.
Abdullahi ya jaddada mahimmancin kashe gobara, inda ya bukaci jama’a da su yi taka tsantsan.