Connect with us

News

Yadda Sabon Farashin Wutar Lantarki Ya Gigita ‘Yan Najeriya

Published

on

Spread the love

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Gwamnatin Najeriya ta sanar karin kudin wutan lantarki da fiye da kaso 300 cikin 100 ga masu amfani da wutar lantarki.

Sabon farashin wutan lantarki da hukumar kula da da harkokin kamfanonin da ke rarraba wutan lantarki ta sanar a Abuja ya nuna cewa gwamnatin ta amincewa kamfanonin su kara kudin wutan ne daga Naira 68 kowane kilowatt na lantarki zuwa Naira 225.

Advertisement

Hukumar Kwastam sun tattara Naira tiriliyan 1 a wata ukun farkon shekara 2024.

Wannan kari ne da ya shafi Masu amfani da wutar lantarkin da ke a birane wadanda ke samun wutan lantarki na sao’i 20 a kowace rana, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar kula da sa ido a harkar wutan lantarki Musliu Oseni ya sanar.

Dw ta ruwaito cewa tuni kungiyar kwadagon Najeiyar ta bayyana rashin amincewarta da wannan kari, inda ta ce za ta yi fito na fito da shi.

Hukumar ta bayyana cewa akwai masu amfani da wutan lantarkin da suke a kaso na daya da a yanzu ta mayara da su kaso na biyu saboda gaza cika kaidar samar masu da wutan lantarki.

Advertisement

An yi karin kudin wutar lantarkin ne a daidai lokacin da al’umman Najeriya ke fama da matsaloli na tsadar rayuwa.

Gwamnatin Najeriya dai ta dade tana koke cewa ba za ta iya ci gaba da samar da tallafi a kan wutar lantarki da ya kai Naira tirliyan 1.3 ita kuma abinda ta kasafta a wannan shekarar shine Naira bilyan 450.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *