Business
Bankin kasa CBN ya sake karya farashin Dalar Amurka domin farfaɗo da darajar Naira.
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Babban bankin kasa CBN ya sanar da sake karya farashin Dalar Amurka a wani yunkurin na sauye-sauye da yake yi domin farfaɗo da darajar Naira.
Za mu gabatar da kudurin kin amincewa da ƙarin kuɗin Wutar lantarki – Sanata Ndume
CBN ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na intanet a Litinin din nan.
Ya ce a yanzu ya shirya sayar da Dala 10,000 ga kowanne kamfanin musayar kudi a kan Naira 1,101.
CBN ya kuma umarci kamfanonin da su sayar da dalar kan karin ribar da ba ta wuce kashi 1.5 cikin 100 kan farashin nasa ba.
Faɗuwar da darajar Nairar ta dinga yi a makonnin da suka gabata ta jawo ɗaukar matakai daban-daban daga bangaren hukumomi ciki har da kama yan kasuwar hada-hadar kudaden ketare da jami’an tsaro suka yi a biranen Kano da Abuja da Legas.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
