Connect with us

News

Rasha ta aike da na’urorin tsaron sama tare da sojoji 100 zuwa Jamhuriyar Nijar

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kasar Rasha ta aike da wani na’urorin tsaron sama da kuma masu horas da sojoji 100 zuwa Jamhuriyar Nijar da ke yammacin Afirka.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Jami’an soji daga ma’aikatar tsaron kasar Rasha za su girka tsarin tare da horas da sojojin Nijar yadda za su yi amfani da na’urorin, kamar yadda kafar yada labarai ta Jamhuriyar Nijar RTN ta ruwaito a yammacin ranar Alhamis.

2024 UTME: Hukumar Jamb ta bukaci dalibai da su fara fitar da takardar shaidar jarabawarsu

Kafin hakan dai an yi wata tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaban gwamnatin mulkin soja Abdourahamane Tchiani da shugaban Rasha Vladimir Putin a karshen watan Maris.

Advertisement

Gidan talabijin din kasar ya nuna hotunan wani jirgin kasar Rasha Ilyushin-76 da ya sauka a filin jirgin saman Yamai ranar Laraba.

Mun zo nan ne don horas da sojojin Nijar wasu manyan makaman yaki da muka zo musu da shi.

Advertisement

Tun bayan juyin mulki da Nijar ta yi a shekarar bara, Kasar ta yi hannun riga da Amurka, Faransa da wasu kasashen turai.

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending