News
2024 UTME: Hukumar Jamb ta bukaci dalibai da su fara fitar da takardar shaidar jarabawarsu
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da Sakandare ta kasa JAMB; ta bukaci dalibai da su fara fitar da takardar shaidar jarabawarsu wato examination notification slip daga shafin website na hukumar daga gobe Talata.
Shugaban sashen yada labarai na hukumar Dr. Fabian Benjamin ne ya bayyana haka ga manema labarai Abuja.
Hukumar NAFDAC ta haramta amfani da maganin tari na yara na kamfanin J&J
Ya ce tuni komai ya gama kankama domin rubuta jarabawar wanda za a fara ranar Juma’a, 19 ga Afrilu
Hukumar ta JAMB ya kuma ce wajibi ne ga duk dalibin da zai rubuta jarabawar da ya tabbatar da cewa ya cire takardar jarabawar daga website din hukumar kafın nan zuwa ranar Juma’a, 19 ga Afrilu., duk kuwa dalibin da ya gaza haka to ya tabbatar da cewa ba zai rubuta jarabawar a bana ba.
Ya kara da cewa, don samun nasarar zana jarabawar, an shawarci wadanda suka shiga jarrabawar da su buga ko kafin ranar Juma’a, 19 ga Afrilu.
Ya bayyana hakan ne domin a ba su damar gano wurin da cibiyar tasu ta kasance, domin hana yin latti a ranar da aka tsara jarabawarsu.
Ku tuna cewa 2024 UTME ta shirya farawa ranar Juma’a, 19 ga Afrilu kuma ya ƙare ranar Litinin, 29 ga
Afrilu.