Entertainment
Karatun Fatiha Ya Jawo Wa Jarumin Tik-Tok G-Fresh Caccaka
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
A wani faifan bidiyo da ya bayyana a makon da ya gabata an hangi Fitaccen ɗan TikTok G-Fresh Al’amin a lokacin bikin sallah inda ya bukaci a karantawa marigayi Saratu Giɗaɗo wacce aka fi sani da Mama Daso suratul Fatiha da nufin Ubangiji ya mata rahama.
To wannan karatun Fatiha dai ya jawo wa wannan jarumi suka da caccaka inda mutane ke ganin cewar ya yiwa Al-Qur’ani izgili ne sakamakon kwantawa da yayi a ƙasa bayan ya gama karatun.
Babbar Magana: Wani Mutum Ya Kashe Matarsa Da Dutsen Guga A Kano
Faruwar wannan lamari bai yiwa mutane da dama daɗi ba inda suke ganin haka a matsayin rashin ɗa’a wanda Hakan ya ja Mutane da dama suka ja hankalin G-Fresh inda suke masa gargaɗin inzai yi shaƙiyancin sa ya yi amma karya sake ya taɓo Qur’ani.
Wikki Time ta ruwaito cewa Kaɗan daga cikin martani mutane
Ibrahim Arif ya ce” Astagfurulla Allah Mun tuba”
Musa Isa shi kuma ya ce” Allah kar ka kama mu da laifin wawayen cikin mu”
Maryam Abba kuwa cewa ta yin ” Yanzu shi a ganin sa wannan abun burgewa ne ko? Ka rasa da me zaka nemi suna sai ta hanyar yiwa addini izgilanci”.