Entertainment
Kamfanin TikTok Zai Kalubalanci Dokar Amrika A Gaban Shari’a
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Kamfanin TikTok ya yi barazanar yin fito na fito a gaban shari’a kan dokar Amirka na son janye kamfani daga zama mallakin kasar Chaina.
A ranar Laraba, Shugaba Joe Biden na Amirka ya sanya hannu kan dokar da ta bai wa mallakin kamfanin na ByteDance wa’adin watanni 9 ya siyar da TikoTok.
Idan har kamfanin ByteDance ya ki siyar da TikTok, zai fuskanci hukuncin janye sa daga manhajojin Apple da kuma Google app store a Amirkar.
Gwamnatin Tarraya Na Tunanin Sakewa Kurkukun Suleja Matsuguni Biyo Bayan Tsaerewar Fursunoni
Ana kuma sa ran masu amfanin da Manhajar TikTok a Amirka miliyan 170 su dauki matakin shari’a kan wannan doka. A watan Nuwanbar 2022 ce dai, wani alkalin Kotun Montana da hana hukuncin haramta TikTok a kasar.
Haka zalika a baya wata kotu ta dakatar da tsohon shugaban kasar Donald Trump daga haramta manhajar.