Connect with us

Entertainment

Yadda Fim din Uku Sau Uku ke cigaba da daukar hankalin masu kallo

Published

on

Spread the love

DAGA IBRAHIM HAMISU

 

Fim din Uku sau Uku fim ne mai dogon zango wanda ake cigaba da ɗorawa a tashar Youtube ta AKA ANFARA

Advertisement

Misbshu Ali da aka fi sani da AKA Amfara shi ne mashiryin shirin kuma shi ne ya fito a matsayin Faisal , ya bayyana dalilan da yasa fim din ke samun karɓuwa a wajen al’umma,

Kungiyar ASUU Ta Dakatar Da Yajin Aikin Gargadi Na Makonni Biyu A Kano

Inda ya ce “Fim din yana taɓo abubuwa da dama da suka taba rayuwar al’umma, idan muka dauki zamantakewar aure ka ga mun taɓo abinda ya shafi auren kisan wuta inda take so na aure ta na kwana 3 ta bani miliyan 3 na yi mata saki uku ka ga anan ya tabo wani abu da ya ke haramun wanda a wannan lokaci da muke ciki za ka ga wasu suna yi”

Ya kara da cewa “Ina godiya ga masu kallonmu wanda su ne suke kara mana kwarin gwiwa wajen jajiecewa mu yi aiki mai inganci

Advertisement

Sannan Ina yi wa ƴan kallon albishir da cewa Fim din uku sau uku zai cigaba da Fadakarwa da nishadantar da masu kallo domin gaskiya muna shiri mai kyau don inganta Fim din”. Inji Misbshu Anfara

Rahama Muhammad wacce aka fi sani da mamar mal. Ali a kwana Casa’in ta ce ta daɗe ba ta yi wani fim da ya yi mata dadi kamar uku sau uku ba, inda ta ce fim din yana nishadantarwa da kuma fadakar da al’umma.

Husaini Ali Muhammad shi ne Daraktan na Fim din Uku Sau Uku kuma shi rubuta labarin ya bayyana cewa fim din ya kunshi darasin rayuwa gaba daya ta yadda duk wanda ya kalla zai karu kuma ya nishadantu,

Advertisement

Ya kara da cewa ” Tunda aka fara yin Fim mai dogon zango a shekarar 2019 ban taba yin fim da ya kai Uku sau Uku ba, gaskiya ina alfahari da shi,

Sannan Fim ne da yake dauke da izna ta rayuwa, domin ko da mutum ba ya jin Hausa idan ya kalli Fim din Uku sau Uku zai karu da darasin rayuwa” ta bakin Darakta Husaini Ali

Fim din wanda a yanzu haka ake dora season 5, a tashar Youtube, ana sa ran dora season 6 a cikin watan 10 na shekarar da muke ciki.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *