Connect with us

News

Yadda ‘Yan ta’adda 200 suka yi wa sojoji diran bazata a sanasanin Faskari

Published

on

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Sojoji 5 ne suka rasu, sannan wasu 11 suka jikkita yayin da yan ta’adda suka kai wa sansanin sojoji dake Faskari hari da yammacin Lahadi.

Advertisement

Haka kuma yan ta’addan sun kashe wani dan banga mai suna tukur Aliyu a wannan hari, kamar yadda sanawar hedikwatar tsaro ta fadi.

Abinda Atiku, Obi, Saraki da Lamido suka tattauna a ganawar sirri da suka yi a Abuja

“Harin ta’addancin da aka kai a sansanin soji ya haifar da munanan raunuka da kuma mutuwar jami’an soji,”

Advertisement

” Lamarin ya faru ne da misalin karfe biyu na rana ranar Lahadi. ‘Yan ta’adda sama da 200 dauke da manyan makamai karkashin jagorancin wani gogarman ‘yan ta’adda mai suna, Ado Aleiru, suka kai hari a sansanin sojoji da ke kauyen ‘Yar Malamai.

“An kwashe sama da sa’o’i biyu ana gwabza kazamin batakashi tsakanin sojoji na kasa da sama, sai dai kuma an rasa sojoji 5 da dan banga daya mai suna Aliyu Tukur mai shekaru 30.

Advertisement

“Sojoji 11 sun samu raunuka daban-daban na harbin bindiga, duk wadanda suka jikkata sojoji sun garzaya da su asibiti, an kuma kwashe gawarwakin duka wadanda suka rasu kamar yanda Jaridar Premium Times ta ruwaito 

“Haka ma ‘yan bindigar sun samu munanan raunuka amma sun yi nasarar kawar da su daga wurin. Bayan haka mazauna yankin na yin hijira a halin yanzu saboda fargabar kada ‘yan ta’addan su yi musu diran ba zata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending