Connect with us

News

Wata Gobara Ta Kashe Jarirari Sabbin Haihuwa Guda Shida

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Rahotanni daga New Delhi babban birnin kasar Indiya, na cewa wata gobara ta tashi a sashen kula da jarirari na wani asibiti, inda ya zuwa yanzu jarirai sabbin haihuwa guda shida suka salwanta.

Advertisement

Sarakunan Da Aka Taba Ciresu Daga Kan Karagar Mulki Sannan Aka Sake Dawo Dasu

Jami’an tsaro musamman na ‘yan sanda sun ce sun ceto wasu jarirai 12 su ma sabbin haihuwa, kuma ana ba su kulawa ta likita.

Jami’an sun kuma ce za a dauki mataki na shari’a a kan mamallakin asibitin, sai dai ba su ba da cikakken dalili ko karin bayani ba.

Advertisement

Cikin daren da ya gabata ne dai gobarar ta tashi, inda wuta ta yi muni saboda fashe-fashen tukwanen iskar Oxygen da ake tallafa wa marasa lafiya da su.

Ba a dai kai ga bayyana musabbabin tashin gobarar ba.

Advertisement

 

DW

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending