News
SHEKARA ƊAYA TA MULKIN ABBA: Kanawa Suna Ganin Sauyi Wajen Samun Kwanciyar Hankali Da Arziki Da Tsaro –Yahya Abdullahi
DAGA KABIR BASIRU FULATAN
Dan Takarar Shugabancin karamar hukumar Kano municipal a Jamiyyar New Nigeria People Party NNPP HON yahya Abdullahi Wanda akafi sani da Baba Mai duniya ya ce Kanawa sun fara tafiya mai kawo sauyi ta fuskar samun kwanciyar hankali da arziki da tsaro a cikin shekara ta farko tun bayan hawan Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf kan kujerar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Mai duniya ya bayyana hakkanne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun,sa ya sanyawa hannu a daren jiya
yace Hakika bayyi mamakin aikace aikace alkhairi da gwamna abba Kabir Yusuf ya aiwatar cikin shekara guda ba duk kuwa kalubalen shariar daya fuskanta a lokacin hawanasa Mulki
Abba ya kasance mai ziciyar yine Kuma Yana kokarin kamanta adalci da gaskiya tun lokacin da yake shugabantar hukumar aiki ta Jahar Kano
A Dan haka mutanan Kano dola ne muyi godiya tare da Kara jinjinawa jagoran kwankwasiyya Dr rabiu Musa kwankwaso Yadda ya kawomana mutum mai kishi wanda Zaiyi adalci wajen jagorancin Al,ummar
Sai dai Kuma Jaridar Inda Ranka ta rawaito wasu daga aiyukan da mai girma Gwamna Engr. Abba Kabir Yusuf ya aywatar cikin Shekara Daya
1. Mayar da jarrabawar WAEC, NECO da NABTEB kyauta ga yan makarantun sakandare.
2. Zabtare kudin makarantun gaba da sakandare da kaso 50 cikin 100
3. Kai dalibai masu hazaka 1001 kasashen waje don digiri na biyu
4. Biyawa daliban wasu daga jami’o’in gwamnatin tarayya kamar su BUK, FUD, da ABU kudin makaranta
5. Fara gyaran makarantun firamare da sakandare da suka lalace a fadin jihar Kano
6. Dawo da makarantu 26 da tsohuwar gwamnati ta rufe.
7. Hadin gwiwa da Bankin Duniya don ci gaban ilimin fasaha da na sana’a wato (Technical and Vocational)
8. Kammala gyaran makarantar Fasahar Sadarwa da ke Kura
9. Samar da tallafin karatu ga daliban gaba da sakandare na jihar Kano
10. Raba fom din jarrabawar JAMB ga dalibai 6,500 yan jihar Kano.
11. Yarda da biyan kudi miliyan 75 domin samar da sababbin kwasa-kwasai (accreditation) a makarantun Polythechnic.
12. Dawo da kwamitin CRC a fadin jihar Kano
MANYAN AIYUKA
13. Aikin rufe babbar kwata daga Jakara zuwa Kwarin Gogau (Wuju-Wuju)
14. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a Dawakin Kudu
15. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a Gwarzo
16. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a Bebeji
17. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a Albasu
18. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a titin Rano zuwa Rurum
19. Aikin titin 5 kilomita mai hannu biyu a Kabo
20. Aikin titin 5 kilomita ta Gezawa
21. Gyaran manyan kwalbatoci biyu da suka hade Rano da Rurum
22. Gyarawa da canja karafan raba titin Katsina road
23. Gyaran gadojin tsallaka titi a kusa da makarantun BUK, Sa’adatu Rimi, Legal, da sauransu.
24. Kammala gadojin tsallaka titi na karfe a Kurna Babban Layi kusa da masallacin Kandahar.
25. Kammala gadar siminti a titin Sheikh Ja’afar, Kwanar Dawaki, Rumfa Kwaleji, da kuma Titin Gwarzo.
26. Gyaran titin Kuntau-Dorayi Babba.
27. Kiyayewa daga zaizayar kasa a gadar Garanga dake Bunkure.
28. Yin kwatoci a unguwar Indabawa da ke Karamar Hukumar Birni.
29. Kammala gyare-gyare a biranen Kwankwasiyya, Amana da Bandirawo
30. Gyaran masallacin Idi.
31. Yin manyan kwalbatoci a Rafin Gora da Rafin Zur da ke Karamar Hukumar Rano
32. Kananun gyararraki a duka titunan jihar Kano
33. Bayar da kwantaragin biliyan uku da miliyan dari shida domin fadada titin Zaria
34. Fara gyaran makarantun Technical a fadin jihar Kano
35. Fara yin gadar kasa a titin Dan Agundi
36. Fara yin titin sama a titin Tal’udu.
37. Fara saka fitulan solar a fadin titunan jihar Kano
38. Gyaran makarantar Bagauda
39. Gyaran sakatariyar Audu Bako
40. Aikin titin Hotoro zuwa Unguwa Uku
41. Fara gyaran duka makarantun koyon sana’a guda 22 a jihar Kano (Vocational Schools).
42. Gyaran gadar Kasa ta Muhammadu Buhari (Kabuga da Kofar Ruwa)
43. Ginin ofisoshi da masallacin mata da dakin taro a hukumar Hisbah.
44. Gyaran hukumar shari’a ta jihar Kano (Law Reform Commission)
45. Ginin gidaje guda takwas da gyaran katangar gidan gwamnatin Kano
46. Ginin bangaren buge-buge na zamani a hukumar ɗab’i ta jihar Kano
47. Sabunta makarantar kiwon dabbobi ta Bagauda.
48. Gyaran titin Bayero-Soli da kuma samar da hanyar shiga a kusa da rukunin gidajen Ado Bayero Mall.
49. Ginin kwalbatin da ta rushe a hanyar Takai-Fajewa – Kayarda – Birnin Bako a karamar hukumar Takai.
50 gyaran gadar nassarawa da kofar gadan Kaya
BANGAREN LAFIYA
51. Bawa yara sama da 200,000 magani kyauta a asibitin Hasiya Bayero
52. Sabunta asibitin Sir Sanusi General Hospital
53. Sabunta asibitin Nuhu Bamalli.
54. Sabunta asibitin BELA
55 Samar da tsarin haihuwa kyauta
56. Yawon duba marasa lafiya a kauyukan jihar Kano
57 Kaddamar da tsarin “Abba Care” don kula da masu cutar sikila a fadin jihar Kano.
58 Gyara da sake ginin asibitin Murtala Muhammad
59Siyan motocin ambulance don amfanin kananan hukumomi
50 Diban ma’aikatan lafiya da likitoci guda 106 a fadin jiha.
61. Daukan manyan likitoci “consultants” don su taimakawa asibitoci wajen samar da lasisin bude wasu ɓangarori kamar ENT, family medicine, gynecology da sauransu.
62 Samar da tsarin gwajin masu niyyar aure don kiyaye lafiyarsu
63 Hadin guiwa da Global Health Partners don zuwa dollar million hamsin cikin shekara uku a harkar lafiyar jihar Kano
64. Hadin gwiwa da gidauniyar Bill and Melinda Gates domin tallafawa harkar lafiya a jihar Kano
65Biya don saka kayan ICU na zamani a asibitin Murtala Muhammad
66. Samar da motocin aiki ga bangarorin lafiya guda uku na jihar Kano
BANGAREN JIN KAI
67. Rarraba hatsi kyauta ga masu karamin karfi, taki da kayan aikin noma ga manoma a jihar don rage tasirin cire tallafin man fetur.
68 Fara kashin farko na na Auren Zaurawa
69 Raba shinkafa da masara 457,000 kilogiram 10 a matayin tallafi ga unguwanni 484 da ke jihar.
70 Shirin ba da tallafi na wata-wata ga mata na basu jarin N50,000 da yanzu ya samarwa mutane 5,200 a fadin jiha.
71 Kashi na 2, na 3 da na 4 na rabon kayan jin kai (palliative) a fadin jihar
72. Rarraba kayan amfanin gona irin su shinkafa da irin masara da akuya da injinan fanfo ruwa ga mata kusan 1000 a jihar.
AIKIN GWAMNATI
73. Biyan duk wasu basussukan kudaden fansho na wadanda suka yi ritaya daga aikin gwamnati na jihar Kano.
74 Dakatar da cirar da ba dole ba daga albashin ma’aikatan jihar da wadanda suka yi ritaya.
75. Biyan kashi na biyu na bashi ga ’yan fansho da gwamnatin da ta shude ta hana biyansu na tsawon shekaru. An ware biliyan biyar don hakan.
76. Buga sakamakon taron majalisar zartarwa na mako-mako a jaridu da shafukan sada-zumunta
77Horowa, sake horarwa, da haɓaka ingantaccen yanayin aiki don haɓaka yawan aiki da haɓaka ingancin sabis.
78. Samar da majalissar biya da bibiyar hakkin yan fanshon da suka mutu.
RUWAN SHA
79 Amincewa da Naira Miliyan 225 don samar da ton 600 na Aluminum Sulfate (Alum) ga ma’aikatun sarrafa ruwa na jihar.
80. Sayan ƙarin injunan bututun ruwa daga Jamus waɗanda za su kasance a matsayin tsarin ajiya idan aka sami lalacewa a nan gaba.
81 Gina rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana a kauyukan Danya da Kyallin Bula da ke karamar hukumar Bichi da Bebeji a jihar Kano bayan shafe shekaru 40 ana fama da karancin ruwa.
82. Aikin gyara na ci gaba a Hukumar Albarkatun Ruwa ta (WRECA), don kammala aikin gyarawa tun daga Tushen Ruwa na Tamburawa.
83. Ci gaba da babban gyara a bangaren tace ruwa na Challawa..
84 Gwamnatin jihar Kano ta cimma matsaya da gwamnatin Faransa na zuba jarin Yuro miliyan 63.4 domin gina kamfanin samar da ruwan sha na Kano karo na uku.
85Gyara magudanar ruwa da ta tarwatse don hana ambaliyar ruwa ta kowace shekara a lokacin damina a fadin jiha.
NOMA
86. Samar da jimillar gidaje 500,000 don cin gajiyar shirye-shiryen Gwamnatin Jiha ta Tallafawa Noma.
87Samar da ingantaccen kayan aikin noma ta hanyar KASCO
88. Kokarin dasa itatuwa miliyan 2.5 a jihar domin dakile tasirin sauyin yanayi
88Dawo da shirin tallafin aiyukan kiwo
90. Gyaran asibitin dabbobi na Gwale
91. Kimanin matasa 200 ne aka horas da su tare da ba su damar gudanar da ayyukan kiwon dabbobi masu zaman kansu a kananan hukumomi 44 na jihar.
92 Haɓaka Cibiyar Insemination na Kadawa, gyara wurin da samar da kayan aiki na zamani.
93. An fara shata shataletalen hanyoyin dabbobi kusan kilomita 1,950 don magance rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya.
94 An tallafa wa mata 2,357 da raguna da tumaki da akuya domin yin kitso da hayayyafa ta hanyar aikin noma na manoma na jihar Kano (KSADP).
95 An baiwa manoman gyada 1,200 ‘Aflasafe’ a karkashin shirin sarkar darajar legumes na KNARDA domin hana asara bayan girbi.
96 Sayan famfunan ruwa guda 2,050 wanda kuma aka baiwa manoman a matsayin wani abin karfafa gwiwa.
97 Gwamnatin jiha a karkashin shirin Agro Processing and Productivity Enhancement and Livelihood Support (APPEALS) na tallafawa manoma 300 akan noman shinkafa, alkama, da noman tumatur
Martaba
98 Kwacewa da gyaran asibitin yara na Hasiya Bayero
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
