Connect with us

News

Yan Majalisa Tarraya Sun Fito Da Ƙudirin Wa’adin Shekaru Shida Ga Shugaban Ƙasa, Gwamnoni 

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Wani gungun ‘Yan Majalisar Tarayya sun fito da ƙuri’in neman sake fasali da tsarin mulkin Najeriya, wanda zai canja wa’adin mulkin shugaban ƙasa da na gwamnoni, daga zango biyu (shekara 4 sau 2) zuwa zango ɗaya mai wa’adin shekaru 6.

Advertisement

Haka nan kuma a cikin ƙudirin, sun bada shawarar kafa dokar maida tsarin shugaban ƙasa zuwa tsari na karɓa-karɓa, tsakanin Arewa da Kudu, sannan kuma sun nemi a ƙirƙiro tsarin mataimakan shugaban ƙasa guda biyu.

Binciken El-Rufai Da Wasu Kusoshin Gwamnatinsa 5

Waɗannan shawarwari dai na daga cikin buƙatu shida da ke cikin ƙudirin, wanda ‘yan majalisar suka bijiro da shi a zauren Majalisar Tarayya, a ranar Litinin.

Advertisement

Premium Times ta ruwaito cewa Da suke wa manema labarai ƙarin bayani a Majalisa ranar Litinin, ‘yan majalisar masu kiran kan su ‘Baraden Sauya Tsarin Mulki’, sun ce wannan ƙudiri na sauya wa’adin mulkin shugaban ƙasa da na gwamnoni da ƙirƙiro ofishin mataimakin shugaban ƙasa guda biyu, an shigar da shi a majalisar tarayya.

Da ya ke magana a madadin sauran gungun ‘yan majalisar, Ikenga Ugochinyere, ɗan PDP daga Jihar Imo, ya ce hakan da suka bijiro wani mataki ne ƙwaƙƙwara wanda zai magance ƙorafe-ƙorafen da ɓangarori da yankunan ƙasar nan ke ta yi tsawon shekara da shekaru.

Advertisement

Ya ce kuma zai rage kashe kuɗaɗe wajen tafiyar da gwamnati, sannan kuma zai ƙara danƙon zumunci tsakanin ɓangarorin ƙasar nan da juna

Ugochinyere wanda ke tare da sauran ‘yan majalisa bakwai masu irin ra’ayin sa da ke cikin guruf ɗin, ya ce ɗaya daga cikin ƙudirin da suka bijiro da shi, “shi ne neman a kafa dokar da za ta ƙirƙiro ofishin mataimakin shugaban ƙasa guda biyu, ɗaya daga Arewa ɗaya kuma daga Kudu.

Advertisement

Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko zai kasance wanda ake zaɓe tare da shugaban ƙasa, kuma wa’adin sa ya ƙare tare da shugaban ƙasa.

“Mataikakin shugaban ƙasa na biyu kuwa zai kasance minista ne wanda shi zai riƙa kula da tattalin arzikin ƙasa. Kuma su biyu ɗin za su kasance duk ministoci ne.”

Advertisement

“Sannan kuma mataimakin shugaban ƙasa na farko zai kasance yankin su ɗaya da shugaban ƙasa, domin tabbatar da samun nasarar tafiyar da gwamnati da kuma miƙa mulki daga wannan gwamnati zuwa wata, salum-alum.”

Sannan kuma sun fito da cewa sun amince kasa Najeriya shiyyoyi shida, domin samar da tsarin karɓa-karɓa a tsakanin shiyyoin shida, wanda hakan a cewar su zai rage ƙumaji da gaganiyar neman mulki afujajan da rage hanƙoron neman kafa ƙarin jihohi.”

Advertisement

Sun kuma bijiro da dokar ƙara tabbatar da ƙarfin ikon cin gashin kan ƙananan hukumomi.

Sun kuma ce za su fito da ƙudirori 50 domin a sake fasalin tsarin kundin dokokin Najeriya.

Advertisement

Sun ce tsarin mulkin dimokraɗiyyar da ake tafiya a kai yanzu, cike ya ce da naƙasu, bauɗiya da cikas a wurare da dama.

Saboda haka sun yi kira a bai wa lamarin buda da hankali bisa gaskiya.

Advertisement

Sun kuma nemi a riƙa yin zaɓukan shugaban ƙasa, gwamnoni, ‘Yan Majalisar Tarayya, Sanatoci da Majalisar Dokokin Jihohi duk a rana ɗaya.

Sun ƙara da cewa kuma tilas a riƙa kammala dukkan shari’un zaɓe kafin ranar rantsar da waɗanda suka yi nasara.

Advertisement

Ya ce mambobin guruf ɗin na su sun kai 35, amma dai mutum takwas ne suka halarci taron manema labaran.

Sun haɗa da Mathew Nwogu, Usaman Balami, Awaji-Inombek, Abiamte da Kanja Abduhamid.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending