News
Binciken El-Rufai Da Wasu Kusoshin Gwamnatinsa 5
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Hukumar EFCC mai yaki da cin hanci da karya tattalin arziki ta kafa wata tawagar kwararru da zasu binciki tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, bisa zargin almundahanar biliyan N423.
Wikki Times ta ruwaito cewa EFCC ta kafa tawagar kwararrun ne domin su gano gaskiya a kan zargin karkatar da N423bn da ake yi wa El-Rufai da wasu manyan jami’an gwamnatinsa da suka rike wasu muhimman mukamai a gwamnatinsa.
Yan Ta,adda Sun Sace Fasinjoji A Babbar Hanyar Maiduguri Zuwa Kano
Ana sa ran tawagar EFCC za ta gayyaci El-Rufai kwanan nan domin ya amsa tambayoyi.
Sauran wadanda za a gayyata domin amsa tambayoyi a kan zargin badakalar kudin sun hada da dukkan wadanda suka taba rike mukamin kwamishinan kudi, babban akawu, da shugabantar hukumar tattara haraji ta jihar Kaduna (KADIRS) a lokacin mulkin El-Rufai.
Ragowar sun hada da tsofin darektocin kamfanin cigaban kasuwannin Kaduna, tsofin shugabanni a hukumar kula da hanyoyin Kaduna in banda Injiniya Amina Ja’afar Ladan, wacce ta rike hukumar na tsawon wata daya kacal a zamanin mulkin El-Rufai.
“Mun karbi takardar korafi daga kungiya mai zaman kan ta (NGO) kuma mun fara bincike akan korafe-korafen da takardar ta kunsa.
“Rahoton kwamitin bincike da majalisar jihar Kaduna ta kafa zai matukar taimakawa kuma nan bada dadewa ba zamu gayyaci El-Rufai da wasu kusoshin gwamnatinsa domin amsa tambayoyi.
“Tawagar da zata yi aikin ta yi zama mai tsawo ranar Litinin (jiya) domin nazartar dukkan batutuwan da ke cikin korafin da muka karba da kuma wanda ke cikin rahoton kwamitin majalisar jihar Kaduna.
“Munn samu muhimman bayanai a rahoton kwamitin majalisa da zasu bamu damar fara aikin mu.” kamar yadda wata majiya ta sanar da jaridar The Nation.
