News
Yan Ta,adda Sun Sace Fasinjoji A Babbar Hanyar Maiduguri Zuwa Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Wasu da ake zargin mayakan kungiyar Boko Haram ne sun tare babbar hanyar Maiduguri zuwa Kano, inda suka yi garkuwa da fasinjoji da dama.
Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa da yammacin jiya Litinin ne masu tada kayar bayan suka tare hanya tsakanin Garin Kuturu da Mannanari da ke kusa da Auno, inda suka yi amfani da karfi wajen sace fasinjojin.
Ranar Dimokuraɗiyyar: Ƴan Nijeriya Fushi Suke Da Shugaba Tinubu
Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya tilastawa daruruwan masu ababen hawa komawa garuwan Benishek da kuma Auno don samun mafaka. a cikinsu, sun shaidawa jaridar cewar basu san adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ba.
Sun ce suna kyautata zaton cewa masu tada kayar bayan sun fito ne don neman kayan abinci, ganin yadda aka kansu dauke da baruka har uku.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
