Business
Mining :masu tapswap sun dage ranar da Zata fashe
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mamallaka manhajar Tapswap da ke mining din ta sun bayyana cewa sun dage ranar kaddamar da ita.
Jarida PUNCH ta ruwaito shugaban sashin sadarwa na kamfanin, John Robbin ne ya bayyana hakan a wata sadarwa da ya fitar.
Matasa da yawa a Nigeria dai sun rungumi Sana,ar mining, tun bayan da wasu matasan suka sami kudade masu Tarin yawa .daga kamfanin Notcoin.
Kafin wannan lokacin a baya kamfanin ya sanar da cewa ranar da zai kaddamar dashi za ta kasance ranar 1 ga Yuli bayan sun kasa gatabar dashi bisa yawan masu yin wasan.
Har Izuwa wannan lokaci kamfanin bai bayyana ranar da zai kaddamar da Tapswap din ba. Wato ranar da Zata fashe ba
daga karshedai Kamfanin ya Kara baiwa kostomonin nasa hakuri tare da karamusu kwarin gwira wajen ganin sun rabautu da samun sakamako Mai kyau
A wani labari Kuma Tsohon babban hafsan sojin ruwa na Najeriya, Rear Admiral Alison ya kai ƙara gaban kotu domin hana tsohuwar mai ɗakinsa Diezani Alison Madueke yin amfani da sunansa.
Madueke ya buƙaci kotu ta bai wa tsohuwar ministan man fetur ɗin umarnin ta koma yin amfani da sunan mahaifinta Agama kasancewar aurensu ya mutu. tsawan lokaci
Ya kuma wallafa a jaridun Najeriya da waɗanda ke Burtaniya inda yake neman tsohuwar matar tasa ta daina amfani da sunansa.
A takardar ƙorafin, Madueke ya ce cigaba da amfani da sunansa haɗari ne ta fuskar shari’a da kuma sha’anin kuɗi musamman yadda take fuskantar shari’a kan aikata laifi a Najeriya da Burtaniya.
Madueke ya ƙara da cewa tsohuwar matar tasa na kunyatar da shi ganin yadda take ci gaba da bayyana kanta a matsayin mai ɗakinsa duk da cewa sun rabu.
