Business
Tsarin Zamanantar Kasuwanci Na TMP Zai Kawo Karshen Kalubale Ga ‘Yan Kasuwa A Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsarin zamanantar da kasuwanci na hukumar kwastom TMP zai magance matsantawa ‘yan kasuwa ta hanyar bin diddigin kayayyakinsu tun daga farkon siyo kayan zuwa kaiwa gare su.
Hakan zai yiwu ne ta hanyar tsarin manhajar tafikar da ayyuka na bai daya na hukumar Kwastom, wata manhaja da za a samar domin lura da dukkan matakan hada hadar kudi da ‘yan kasuwa zasu yi da hukumar.
Ya Kamata Mata Su Daina Shiga Masana’antar Kannywood –Hadiza Gabon
Tsarin TMP dai hanya ce ta amfani da fasahar zamani na hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya domin saukakawa da kuma taimakawa masu ruwa da tsaki wajen gudanar da kasuwanci cikin sauki.
Haka kuma an samar da tsarin domin samun sahalewar shigo da kayayyaki da fita dasu da biyan harajin kayayyaki cikin sauki.
Tsarin na TMP na hukumar kwastom zai kasance bisa matakai 3 na yarjejeni da zata kai shekaru 20.
An sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar 27 ga watan Mayu na 2023 tsakanin gwamnatin tarayya ta hanyar wakilcin hukumar gudanarwa ta hukumar hana fasa kwauri ta kasa da kamfanin zamanantar da kasuwanci.
CSC Usman Abba wanda shi ne shugaban sashin kula da shirin ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Alhamis cewa ta hanyar amfani da manhajar ‘yan kasuwa zasu iya sanin ko a samu akasi ko matsala a hada hadar kudade da hukumar.
Abba ya ce tsarin zai magance ayyukan bata gari da tona asirin wadanda ake amfani da dama wajen cutar da abokan kasuwancinsu da baza su iya duba kayayyakinsu ba.
“Wannan shafi ne inda dan kasuwa yake da damar shiga kuma zai iya bibiyar dukkan matakan hada hadar kudi da kuma sanin halin da kayansa ke ciki har zuwa lokacin da zasu isa gare shi”, inji shi.
Ya ce hukumar kwastom ta samu rahotanni da dama kan yadda wakilan masu kaya suke yunkurin karbar karin kudade ga abokan huldarsu ta hanyar yi musu karyar ba a sahale musu shiga ko fitar da kayan ba.
Acewarsa, manhajar wacce za a kaddamar kwanan nan an tsara zata dauki dukkan bayanai ciki har da hada hadar bihan kudi da sahale shigo da kaya wacce zata baiwa dan kasuwa damar yin abinda a ka bukata.
“Don haka dan kasuwa zai iya shiga yaga adadin kayan, kuma bayan ya biya kudi ta hanyar manhajar zai gani cewa ya biya da kuma adadin kudin da aka biya.
” Zai iya ganinma cewa kayan ya bar tashar jirgin ruwa saboda muna da shedar amincewa ta wucewa.
“Hakan na nufin idan motar kaya ta fita, manhajar zata nuna cewa motar ta fita”, inji shi.
Sannan ya kara da cewa an shigar da sauran hukumomi cikin manhajar domin duba kayayyaki kamar yadda dokar kasa ta basu dama.
Dangane da yanayin da ake ciki a yanzu haka na samar da manhajar, Abba ya ce an samar da dukkan abinda ake bukata a cikin manhjar sannan ana shigar da bayanan karshe na sanya masu ruwa da tsaki.
” Abinda muke yi na matakin farko shi ne shigar da bayanan masu ruwa da tsaki. Mun kammala da na hukumar kwastom, yanzu muna na masu ruwa da tsaki da kuma nuna musu manhajar da yadda za a shigar dasu.
“Mun tattauna da babban bankin Najeriya CBN da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, saura kiris mun kammala”, inji shi.
Tsarin dai na TMP ana saran zai samar da harajin Dala Biliyan 250 cikin shekaru 20 da aka kayyade masa.
Shirin an samar da shi ne domin sanya Nigeria kan gaba a fannin ci gaban fasahar zamani da kasuwancin kasa da kasa.
Haka kuma zai taimakawa Gwamnatin tarayya na cimma burin bunkasa tattalin arziki ta hanyar kasuwancin kasa da kasa.