Entertainment
Ya Kamata Mata Su Daina Shiga Masana’antar Kannywood –Hadiza Gabon
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood Hadiza Gabon ta bukaci mata da su daina shiga masana’antar Kannywood, inda ta bayyana cewa illar shiga masana’antar da mata ke fuskanta ya fi alfanu dake cikin masana’antar.
Hadiza Gabon ta bayyana haka ne a wata hira da ta yi a shirinta na tattaunawa, wanda ake watsawa a tashar ta ta YouTube wanda Jaridar INDA RANKA ta sa ido akai
Tur Ka Tur Ka: Wata Mata Ta Kashe Ragon Laiya Da Muciya Saboda Yacinye Ƙullun Ƙosai.
Gabon ta yi wadannan kalamai ne ga bakuwarta, Fitacciyar jarumar fina-finan Kannywood, Surayya Aminu, wadda aka fi sani da Rayya, a lokacin da ta karbi bakuncin ta a cikin shirin.
Gabon ta shaida wa Surayya Aminu cewa, “Idan mace ta zo mini ta ce tana son shiga Kannywood, zan ba ta shawarar ta daina. Idan ta dage sai na yi mata fatan alheri. Amma ina gaya muku, ya fi kyau mace ta yi aiki tuƙuru, ta yi karatu, ta yi aure.”