Entertainment
An Tura Tiktoker Gidan Yari Bayan Kiran Zanga-zanga A kan Halin Kunci Da Ake Ciki A Najeriya
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
An tsare wani dan Najeriya Junaidu Abdullahi aka Sani da Abusalma, a gidan yari bayan ya yada wani faifan bidiyo a shafinsa na TikTok yana kira ga jama’a da su yi zanga-zanga saboda halin kunci da ake ciki a Najeriya
Rahotanni na nuni da cewa an yi zargin jami’an tsaro ne suka dauke Abusalma a ranar Laraba sannan suka tafi da shi Abuja.
Da yake tabbatar da lamarin ga Jaridar DAILY NIGERIAN dan uwan Abusalma, Mustapha Hamza, ya ce Tiktoker a yanzu haka yana tsare a gidan yarin Kurmawa da ke Kano.
“Ya bar gida cikin gaggawa a safiyar Laraba bayan an yi masa kira na gaggawa da misalin karfe 8:30 na safe. Ya fice ba tare da ko breakfast ba. Wannan shine karo na karshe da danginsa suka ganshi.
“Mun kai rahoton lamarin ga ofishin ‘yan sanda, kuma nan take suka buga waya a rediyo, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya bace.
“A yayin da muke ci gaba da neman inda yake, sai aka kira ni a jiya (Juma’a) da misalin karfe 5:30 na yamma, wanda ya kira ni ya sanar da ni cewa Junaidu yana gidan yarin Kurmawa a Kano. Ya kuma bayyana cewa kotu mai lamba 38 dake titin Zungeru Kano ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi tare da dage sauraron karar har sai bayan sati uku.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa, Tiktoker din ya yi wani faifan bidiyo kwanan nan, yana mai cewa duk wani malamin addinin Musulunci da ya yi magana kan zanga-zangar da aka shirya yi to a sauke shi daga kan minbari.
Amma bayan kwana biyu da saka bidiyon, Abusalma ya goge shi tare da neman gafarar malaman addinin musulunci.
Ya kuma yi kira ga jama’a da su guji zanga-zangar domin hakan na iya haifar da tabarbarewar doka da oda.