Entertainment
Ban Ji Ko ‘Dar’ Ba Game Da Goge Shafin Facebook Dina Ba —Rarara
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Fitaccen mawakin nan dan arewacin Najeriya mai suna Dauda Kahutu Rarara ya ce ban ji ko ‘dar’ ba game da goge shafin Facebook dina ba.
A hira da ya yi da tashar DCL a yanar gizo, Rarara ya jero wasu abubuwa da Tinubu ya yi wa ƴan Arewa a tsawon shekara ɗaya da ɗarewa karagar mulkin Najeriya.
Rarara ya kara da cewa duk da dakatar masa da shafinsa ta Facebook da Meta ta yi, ya buɗe wata sabuwar shafi inda tuni har ya fara saka abubuwarsa a ciki.
” Bayan haka manita kanta wancan shafin da aka dakatar, muna nan nuna duba yadda zara dawo aiki.
Daga nan sai Rarara ya ce maganar yi wa Tinubu Zanga-zanga bai ma taso ba ga duk wani ɗan Arewa mai kishin Arewa.
” Tinubu ne fa ya kirkiro wa yankin Arewa Maso Yamma hukumar raya yankin, shugabannin kasa Ƴan Arewa nawa aka yi ba su yi haka ba, Tinubu ya tabbatar da an dawo wa ƙananan hukumomi da martabar su,an kwato musu ƴanci daga gwamnatocin jihohi.
” Kuma duka waɗannan ba Zanga-zanga aka yi masa ba kafin ya aiwatar da haka. Haka kuma ya saka hannu a hukumar ayyukan gona da dabbobi, wanda kowa ya san wannan abu ne da ya shafi Arewa.
” Idan waɗannan hukumomi suka fara aiki, kananan hukumomi suka fara amsar kuɗaɗen su daga gwamnatin tarayya kai tsaye, za ka ga duk matsalolin da ake fama da su sun wanye.
Ya ce mutanen karkara za su rika samun aikin cigaba kamar yadda aka rika yi a baya.
Rahotannin sun bayyana cewa mabiya Rarara a shafin sada zumunta na Facebook da yawa sun tura sakonnin neman a cire shafin mawakin daga dandalin, saboda wata wakar yabo da ya yi wa gwamnatin Najeriya kwanan nan.
Matakin cire shafin dai na zuwa ne bayan da Rarara ya wallafa wata waka ta yabon shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu saboda yadda yake magance matsalolin talauci da tsaro a Najeriya.
A ranar Asabar ne dai aka cire shafin sada zumuntar mawakin na Facebook, wanda ke da mabiya sama da miliyan daya. Wakar da mawakin ya yi ta yaba wa Tinubu kan yadda ya ke kawar da yunwa da rashin tsaro a Arewacin kasar, a cewarsa “yanzu ‘yan Arewa sun yi bankwana da yunwa, rashin tsaro, da talauci.”
Wakar, wadda ta janyo cece-ku-ce dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da zanga-zangar gama-gari daga ranar daya ga watan Agusta, sakamakon tashin farashin abinci da kuma tabarbarewar tattalin arziki a kasar da ta fi yawan jama’a a nahiyar Afrika.
Duk da yabon da Rarara ya ke wa gwamnatin, a kwanan nan sai da mahaifiyarsa ta yi kusan Sati uku a hannun ‘yan bindiga, kafin daga baya suka sako ta.