Connect with us

News

YANZU YANZU: Kotu Ta Dakatar Da Cigaba Da Sauraren Karar Da Wani Matashi Ya Shigar Da  Rarara Kan Sukar Buhari 

Published

on

Spread the love

DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO 

Wata Babbar Kotun Jihar Nasarawa dake zamanta a Doma ta dakatar da Kotun Majistire ta 1 dake Lafia daga ci gaba da sauraren karar da wani matashi Sani Ahmad Zangina ya shigar da fitaccen mawakin Siyasa a Najeriya Dauda Abdullahi Kahutu Rarara kan sukar tsohon shugaban Kasa Muhammad Buhari.

Lauyan dake jagorantar tawagar lauyoyin Rarara Barrister A. I Ma’aji ya bayyanawa wakilin jaridar Tambari cewar sun daukaka kara a gaban kotun Justice Abdullahi H. shamsu Shama na Babbar Kotu dake Doma tun ranar Litinin karshen watan jiya, bisa rashin gamsuwa da umarnin Kotun Majistire da ta tilasta sai Lallai Rarara ya bayyana a gabanta.

Kotu tabayar da belin Abdulmajeed Dan bilki kwamanda bisa wasu sharruda.

Sai dai Lauyan dake wakiltar mai shigar da kara Barista Isah Hassan Nalaraba, ya ce ba su da masaniyar ɗaukaka karar da su ka yi, abin da kawai ya sani shi ne, akwai zaman kotun ranar juma’a.

Advertisement

Idan za a iya tunawa dai kotun kotun Majistire dake Lafia ta sanya ranar juma’a 2 ga watan Fabrairu 2024 a matsayin ranar da za a ci gaban da sauraren karar.

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *