Connect with us

News

Kotu tabayar da belin Abdulmajeed Dan bilki kwamanda bisa wasu sharruda.

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Kotun majistire mai 32, dake zaman ta a unguwar Norman’Sland Kano, karkashin jagorancin mai shari’a Abdul’aziz Habib, ta bayar da belin dan siyasar nan Dan bilki Kwamanda.

Advertisement

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa ana zargin Dan bilki Kwamanda, da laifin furta wasu kalamai da za su iya haifar da rudani ga al’umma, musamman kan abunda ya shafi masarautun jahar Kano guda Biyar.

Yadda Aka Kama Masu Garkuwa Da Mutane 4 A Kano Bayan Karbar Kudin Fansa A Jihar Edo

Sharudan Belin da kotun ta gidanya  sun hada da mutane biyu da za su tsaya masa, wajibi ne kuma daya ya zama babban sakataren gwamnatin jahar Kano da kuma Hakimi.

Advertisement

Haka zalika su a ajiye kudi naira miliyan daya da hotunan su harda na wanda ake zargin.

Mai shari’a Abdul’aziz Habib ya dage ci gaba da sauraren shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Fabarairun 2024 , don ci gaba da sauraren shari’ar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending