Connect with us

News

Kotu Ta Tsare Wani Saurayi Da Budurwa A Gidan Gyaran Hali A Kano

Published

on

DAGA MARYAM BASHIR MUSA

 

Advertisement

Wata babbar kotun majistare da ke zamanta a Kano, a ranar Alhamis, ta bayar da umarnin tsare Aliyu Yakubu mai shekaru 24 da Aisha Sani, 19, a gidan gyaran hali bisa zargin yin zina.

Mutanen biyu da ke zaune a  Hotoro Yandodo Quarters Kano, ana tuhumar su da laifin hada baki da zina.

Advertisement

YANZU YANZU: Kotu Ta Dakatar Da Cigaba Da Sauraren Karar Da Wani Matashi Ya Shigar Da  Rarara Kan Sukar Buhari 

Mai gabatar da kara, Miss Khadija Aliyu, ta shaida wa kotun cewa wadanda ake tuhumar sun aikata laifin ne a shekarar 2023, a Hotoro Quarters Kano.

Ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun hada baki ne a tsakaninsu, inda suka yi lalata da juna.

Advertisement

A cewar mai gabatar da kara, laifin ya ci karo da sashe na 97, 387 da 388 na kundin laifuffuka.

Wadanda ake tuhumar sun amsa laifin da ake tuhumar su da aikatawa.

Advertisement

Alkalin kotun Fauziyya Isa-Sheshe, ta bayar da umarnin a garkame wadanda ake kara a gidan gyaran hali.

Isa-Sheshe ta dage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 8 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci.

Advertisement

 

 

Advertisement

PRIME TIME NEWS 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending