News
Ranar Cutar Kuturta ta Duniya: Gwamnatin jihar Kano ta gyara tsohon asibitin kuturta na Yadakunya tare da kula da majinyata 333
DAGA NUASIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Gwamnatin jihar Kano ta ce ta gyara asibitin kutare da ke Yadakunya, a wani bangare na kokarin tallafa wa mutanen da ke fama da cutar.
Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf ne ya bayyana hakan a asibitin na Yadakunya, a wani yunkuri na gwamnati na tunawa da ranar kuturta ta duniya ta shekarar 2024.
Kotu Ta Tsare Wani Saurayi Da Budurwa A Gidan Gyaran Hali A Kano
Ya ce nuna wariya ga mutanen da kuturta ta kama da iyalansu har yanzu babban kalubale ne, ya kuma yi kira ga mazauna Kano da su kawar da labarin cewar cutar na iya yaduwa.
Bugu da kari, Dakta Labaran ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta fi ba da muhimmanci ga mutanen da ke fama da cutar kuturta, don haka ne ma aka gyara asibitin Yadakunya.
“Tun farkon zuwan mu zuwa yau, an gyara asibitin kuturta na Yadakunya tare da kula da majinyata 333, kuma mun samar da rijiyoyin burtsatse masu amfani da hasken rana, da wutar lantarki da kuma motar daukar marasa lafiya ta asibiti don taimaka wa marasa lafiya.
“Kamar yadda kuka sani, masu fama da kuturta sun cancanci soyayya, kulawa, da sauran gata kamar sauran halittun Allah, sannan kuma ku gargadi jama’a da su guji kyamar wannan nau’i na daidaikun mutane da ma sauran nakasassu,” in ji Dakta Labaran.
Da yake jawabi tun da farko, shugaban kungiyar masu fama da cutar, Malam Isyaku Muhammad, ya yaba da matakan da gwamnatin jihar ta dauka a asibitin wanda ya taimaka kwarai wajen tafiyar da al’amuransu.
Kuturta na cikin jerin cutukan da suka fi yawa a ƙasashemn da ke fama da zafi inda kuma ba a damu da yaɗuwarta ba.
Kuma duk da kokari da hukumomi da sauran ƙungiyoyi ke yi wajen yaƙar cutar, bayanai na cewa har yanzu ana fama da ita, kuma samun magani wani babban ƙalubale ne ga masu ɗauke da cutar
Masana na cewa kuturta har yanzu barazana ce ga duniya musamman ma Afirka da aka bayyana cutar ta fi yaɗuwa.
Alƙumma sun ce kimanin mutum dubu ɗari da saba’in da huɗu suka kamu da cutar a duniya, kuma daga ciki mutum dubu ashirin da ɗaya da ɗari tara da talatin da biyar ƴan Afirka ne.
Taken ranar cutar kuturta ta duniya ta shekarar 2024 ita ce, ‘kayar da cutar kuturta’, don kawar da kyama da ke da alaka da kamuwa da cutar, da kuma wayar da kan jama’a game da hakan.
