Connect with us

News

Babu wata matsala tattare da yarjejeniyar SAMOA — Kungiyar lauyoyin Nijeriya

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

Shugaban kungiyar lauyoyin Najeriya (NBA), Mista Yakubu Maikyau (SAN), ya ce babu wani abu a cikin yarjejeniyar Samoa da ta tilastawa Najeriya amincewa da ‘yancin ‘yan Madigo, Luwadi, Bisexual, Transgender da Queer (LGBTQ).

A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaran Kungiyar NBA na kasa, Mista Habeeb Lawal, Maikyau ya yi gargadi game da munanan labaran da ke tasowa daga bayanan karya kan yarjejeniyar.

Ya ce: “ Hankalina ya karkata ga yadda ake buga jaridu da kafafen sada zumunta na zamani, game da martanin da wasu ‘yan Najeriya suka yi, game da rattaba hannu kan yarjejeniyar SAMOA da gwamnatin tarayya ta yi.

“Sabanin labarin da ake yadawa ko dai saboda rashin sanin abin da yarjejeniyar ta kunsa ko kuma da gangan na yaudarar jama’a,.

“Wannan babu wani tanadi a cikin yarjejeniyar Samoa da ta bukaci Najeriya ta amince ko ta kowace hanya ta amince da LGBTQ ko ‘yan luwadi, ko dai a matsayin wani sharadi na bashi dala biliyan 150 ko kwata-kwata.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending