News
Da Dumi-Dumi :Majalisar Wakilan Nijeriya Ta Bukaci Ayi Gaggawar Dakatar Da Yarjejeniyar SAMOA
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Majalisar Wakilan Nijeriya ta bukaci gwamnatin Tinubu ta yi gaggawar dakatar da yarjejeniyar SAMOA da ta haifar da cece-kuce da zargin taba martabar addini da al’adun mutanen Nijeriya.
Majalisar ta kuma yanke shawarar bincikar yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta rattabawa hannu a ranar 28 ga watan Yuni.
Babu wata matsala tattare da yarjejeniyar SAMOA — Kungiyar lauyoyin Nijeriya
An zartar da kudurin ne biyo bayan amincewa da kudirin gaggawa na Ali Sani Madaki, sashin marasa rinjaye, da wasu ‘yan majalisa 87 suka dauki nauyi.
Kwanan nan yarjejeniyar ta haifar da cece-kuce saboda rahotannin cewa an shigar da tanade-tanade da suka shafi ‘yan madigo, ‘yan luwadi, bisexual, da transgender (LGBT) a cikin yarjejeniyar.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
