News
Ramuwar Gayya :Tsananin Azaba Ta Sa Wani Mutum Rama Cizon Maciji
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wani Ba’indiye mai suna Santosh Lohar ya Gantsarawa wani maciji cizo har lahira a matsayin ramuwar gayya bayan da Maciji ya cije shi yana tsaka da bacci .
WIKKI TIMES ta ruwaito cewa Santosh Dan shekaru 35 daga garin Pandua, Jharkhand a Indiya, yana tsaka da barci wani Maciji ya rarrafo ya gasa masa cizo, nan take kuwa Santosh ya damƙo Maciji da sanda inda shima ya gasa masa cizo.
Lokacin da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya ciji macijin, Lohar ya gaya bayyana cewa: ‘A ƙauyen mu mun yadda cewa idan Maciji ya cije ka to ka kama shi ka cije shi sau biyu don kashe dafin”.
Ya kara da cewa rama cizon da yayi shi ne ya hana shi mutuwa, kasancewar hakan wani canfine da sukayi imani da shi a yankin su.
Duk da da ba gama gane wane irin Maciji ne ya sari Lohar ba. Ba a tsaya ba aka garzaya da shi asibiti da ke kusa da su inda aka ba shi maganin kashe dafin aka sallame shi washegari.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
