Connect with us

Politics

Duk Dan Jamiyyar APC Barawo Ne Bai Kamata A Bashi Aure Ba —Sharfaddin Kantin Kwari

Published

on

1723827959970

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Wani Jigo a Jamiyyar Adawa ta PDP sharfaddin Kantin Kwari ya ce duk wani dan Jamiyyar APC  barawo ne kuma ko ya zo neman Aure kada ku sake ku bashi domin basuda imani balle tausayi kona sisin kwabo.

Advertisement

Sharfaddin Kantin kwari ya bayyana hakan a wata hirar da akayi dashi a cikin Shirin siyasa ALLON KARFE na gidan radiyon Hikima.

Zaben Kananan Hukumomi A Kano: Kora Da Hali Hukumar Zabe Ke Yi Mana – Jam’iyyun Adawa

sharfaddin ya ce bai kamata ace duk wani Uban kirki da ya raini Yarinyar sa Kuma ya bata Tarbiyya har tsowan shekara da shekaru ya dauki yar sa da hannuwan sa ya baiwa dan Jamiyyar APC.

Advertisement

Haka zalika ya kara da cewa koda kafin Auren  ya kamata Iyaye kukoyi yin  buncike  akan Jamiyyar mutum idan ya kasance dan Jamiyyar APC ne kada ku sake ku bashi Auren Yar ku dan basu chanchanci a basu aure ba.

sharfaddin ya Kuma alakanta tabarbarewar  tsaron da Ake fama dashi  a Arewacin Najeriya saboda  rashin imani da rashin tausayi irin na Yayan Jamiyyar APC.

Advertisement

“A baya Kasar mu Najeriya anada tarin arziki amma  yanzu duk sun debe kudin daga su sai Iyalan su babu ruwan su da halin da Yan Najeriya zasu shiga.”

Sharfaddin ya ce a irin wannan lokaci ne da talakawan Najeriya ke fama da halin kuncin rayuwa kuma a daidai  lokacin ne Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ke siyo sabon Jirgin Sama.

Advertisement

sharfaddin ya kara da cewa yana baiwa duk wani dan Jamiyyar APC da zai dauko tallan Tinubu a shekarar 2027 shawar   ya tabbatar ya taho da Rigar kwano domin yanzu talakawa sun gane asalin  gaskiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending