Connect with us

Politics

Ina Jiran Lokaci Domin Allah Shine Mai Bada Mulki —Hon Saddam

Published

on

Dan Takarar Shugabancin karamar hukumar Rogo Jamiyyar New Nigeria People Party NNPP HON Saddam Sani Umar Fulatan

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

Dan Takarar Shugabancin karamar hukumar Rogo Jamiyyar New Nigeria People Party NNPP HON Saddam Sani Umar Fulatan ya ce yana jiran lokaci domin allah shine mai bada mulki ga wanda ya keso.

Jaridar INDA RANKA ta ruwaito cewa, yayin da a ke tunkarar kakar zaɓen Shugabancin kanan Hukumomi da na kansiloli a jihar kano ƴan takara da dama na Jamiyyar NNPP a karamar hukumar Rogo na nuna buƙatar su ta tsayawa domin wakilci na al’ummar karamar hukumar su.

KANO: Matasa Sun Fasa Rumbun Ajiya Inda Suka Kwashi Shinkafa Dake Da Hatimin Gwamnatin Tarayya

Sai dai kuma, rahotanni na nuni da cewa kawo yanzu, ba a ga wata alama da ta nuna cewa dan takarar bazaiyi nassara ba a wannan lokacin.

Amma, a wani shirin tattaunawa da Jaridar INDA RANKA an jiyo Saddam na cewa ita magana ta siyasa ko muƙami, abu ne da Allah ne ya ke yi.

A cewar Saddam , ban da Allah, babu wanda zai iya baiwa wani muƙami, inda ya ƙara da cewa duk wanda ya kaɗai kugen siyasa da wuri ya san Allah ne ke yi, haka-zalika wanda ya jira sai nan gaba shima ya san Allah ne ke yi.

Advertisement

“Ita maganar siyasa ko maganar muƙami, kowa dai ya san Allah ne Ya ke yi. Banda Allah ba bu mai yi kuma a Jira kwai lokaci.

“Wanda ya buga kugen sa da wuri ya sani, wanda kuma ya bari ya jira lokacin Allah, shima kuma ya sani.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending