Politics
Babu ƙofar juyin mulki, ku nemi wata hanyar sauya Gwamnatin Tinubu – Adams Oshiomhole yagayawa ƴan Najeriya
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Sanatan Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, a ranar Laraba ya bayyana cewa babu wata dama da Sojoji za su kwace Mulki a Najeriya.
Oshiomhole ya ce ba zai yuwu wata ƙungiya mara tasiri ba ta nemi sauya tsarin Shugabanci ba a Najeriya.
Wasu masu zanga-zanga da ke fafutukar kawo ƙarshen Mulkin rashin adalci a Najeriya sun bukaci a kori Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda halin kuncin da ƙasar ke ciki.
Sai dai da yake zantawa da manema labarai jigon na Jam’iyyar APC ya ce “Babu yadda za a yi a canza Gwamnati ko kuma Sojoji suyi juyin Mulki, Ba zai yuwu wata kungiya mai ra’ayin rikau ta buƙaci a sauya tsarin Mulki ba.
“Na yaba da hakurin da Tinubu ya yi da yadda ya magance waɗancan batutuwa, inda Tinubu ya bayyanawa ƴan Najeriya cewa na saurare ku, kuma na ji matsalolin ku, amma zan so ganin mun aiwatar da tsare-tsaren mu domin hakan zai magance yunwar da ake fama da ita.
Babu wani lokaci da na yi kira da a sauya Gwamnati a cikin zanga-zangar da na yi, yanzu ina ganin ƴan Siyasa ne ke ƙoƙarin yin uwa makarɓiya da wannan lamari na zanga-zanga.
“Za a iya amfani da zanga-zangar lumana don neman canjin tsarin mulki amma ba canjin Gwamnati ba,” inji shi.
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
