Connect with us

News

Ƴan bindiga sun karbi kudin fansa sunƙi bayar da gawar Sarkin Gobir

Published

on

1724256208139

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

 

Masarautar Sabon Birnin Gobir a jihar Sakkwato ta tabbatar sako ɗan marigayi Sarkin Gobir Alhaji Muhammad Bawa Isa da aka sace su tare mai suna Kabir.

Wani mai magana da yawun  masarautar Alhaji Shuaibu Gwanda Gobir ya ce an sako shi ne da daren jiya bayan biyan waɗanda suka yi garkuwa da shi da Masarautarkuma mahaifinsa kuɗin fansar da suka bukata, amma sun ƙi bayar da gawar mahaifinsa inda suka ce sun riga sun binne shi.

 

Advertisement

Yanzu haka dai ɗan nasa na can na karɓar magani a asibiti a birnin Sakkwato. Magajin Garin na Sabon Birni ya Kuma yace za su yi wa marigayi Sarkin Gobir jana’iza daga nesa wato salatul Ga’ib a yau.

 

Ya buƙaci al’ummar Musulmi a duk duniya da su bi sawunsu wajen yi masa sallar wadda ya ce za su yau.

 

Idan ba,amantaba jaridar Inda ranka ta rawaito cewa Yan bindinga sunyi garkuwa da Sarkin Gobir dashi da Dansa wanda shine Direban da yake Jan motar Sarkin a lokacin, bayan wani taro daya raka mahaifinnasu.

 

Advertisement

 

 

 

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending