News
Gwamnatin Shugaba Tinubu Ta Kara Kudin “Passport”
DAGA KABIRI BASIRU FULATAN
Gwamnatin tarayya ta sanar da karin kudaden karbar Passport din Najeriya daga ranar 1 ga Satumba, 2024.
Hakan ya fito ne ta bakin mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasa (NIS), DCI Kenneth Udo, a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.
Kotun Ingila Ta Ba Kamfanin Chana Iznin Ƙwace Kadarorin Najeriya Biyu A Landan
A cewarsa, daidaita kudaden na daga cikin kokarin gwamnati na tabbatar da inganci da tsaron Passport din Najeriya.
Yanzu farashin “passport” da ake yi N35,000 mai shafuka 32 na tsawon shekaru 5 ya koma N50,000. Sai kuma “passport” mai shafuka 62 na shekaru 10, ya tashi N70,000, ya koma N100,000.
-
News2 days agoWani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
