News
Kotun Ingila Ta Ba Kamfanin Chana Iznin Ƙwace Kadarorin Najeriya Biyu A Landan
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Yadda kotun Ingila ta ba kamfanin Chana iznin ƙwace kadarorin Najeriya biyu a Landan
Cikin watan Yuni ne Babbar Kotun Ingila da ke birnin Landan ta bai wa kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment na Chana iznin riƙe wasu kadarori biyu mallakar gwamnatin Najeriya.
Yan Bindiga Sun kashe Sarkin Gobir bayan garkuwa dashi tsawan Makonni Uku
Gidajen biyu waɗanda Zhongshan ya nemi kotun ta mallaka masa, ɗaya ya na lamba 15 kan Titin Aigburth Hall, a garin Liverpool, sai kuma wani gidan saukar baƙi na Gwamnatin Najeriya, mai suna Beech Lodge, wanda ke lamba 49, Calderstones Road, shi ma a garin Liverpool.
Kamfanin Zongshan ya bayyana wa Babbar Kotun Ingila cewa ɗaya gidan zai iya kai fam miliyan 1.3, ɗayan kuma darajar sa shi ma za ta kai fam miliyan 1.7.
A ranar 14 ga Yuni ne Mai Shari’a Master Sullivan na Babbar Kotun Ingila da ke Landan, ta fitar da wannan hukunci, kamar yadda wasu kwafen takardun da PREMIUM TIMES ta ci karo da su suka tabbatar.
Najeriya ta nuna rashin amincewa, inda ta nuna wa kotu cewa ba a bi ƙa’ida wajen shigar da ƙarar ba. Domin a cewar Najeriya gidajen biyu su na da dokar kariya, kasancewa duk ofisoshin wucin-gadi ne na Ofishin Jakadancin Najeriya da ke Ingila.
Sai dai Mai Shari’a ya ce babu inda aka kawo hujjar cewa gidajen biyu ofishin diflomasiyyar Najeriya ne.
An bai wa kamfanin iznin ƙwace gidajen, biyo bayan gargaɗin ƙarshe da aka ba Najeriya na biyan diyyar Dala miliyan 70 ga Zhongshan, saboda karya sharuɗɗan yarjejeniyar kwangila.
An fara shigar da ƙarar tun a ranar 26 ga Maris, 2021, inda kotu ta umarci Najeriya ta biya diyyar Dala miliyan 55.67. Sai kuma ƙarin kuɗin ruwa na Dala miliyan 9.4.
Ana cikin wannan kwatagwangwamar ce kuma sai Kotun Faransa ta bai wa Zhongshan iznin riƙe jiragen Shugaban Najeriya guda uku da ke filin jirgin Faris, waɗanda aka kai domin yi masu garambawul.
Sai dai kuma cikin makon da ya gabata, Jaridar INDA RANKA ta buga labarin yadda Zhongshan ya saki jirgi ɗaya, a matsayin abinda ya kira, ganin ƙimar Shugaban Najeriya Bola Tinubu, domin jirgin zai hau ya kai ziyara Faransa.
