Connect with us

News

Yan Bindiga Sun kashe Sarkin Gobir bayan garkuwa dashi tsawan Makonni Uku

Published

on

1724256208139

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

 

Bayanai daga makusantan marigayi Sarkin Gobir, Alhaji Isa Muhammad Bawa sun ce an tabbatar da rasuwar Mai Martaban Sarkin bayan Yan bindinga sunyi garkuwa dashi tsawon Makonni Uku.

 

 

Advertisement

Ta cikin wata tattaunawar wayar Talho da kafar yada labarai ta DW Hausa tayi da guda cikin Yayansa wadan da dashi ne aka kai kudin fansa domin cetoshi inda yace sun  iska cewa ‘yan bindigar sun riga da sun harbe shi.

 

Yace Yan bindingar tunda fari sun bukaci da abasu naira million 60 kudin fansa da Kuma mashina hawa guda 5 domin sakin mahaifinnasu.

 

A cewarsa sunso tunda fari su hada kudin fansar a matsayin su na iyalan Sarkin tom amma sai Gwamnati tace zata biya kudin fansar mahaifinnasu.

 

Advertisement

Dan Sarkin Gobir din ya Kara da cewa daga busani ne da suka kai Kudin fansar da La,asar din jiya anan ne suka tabbatar da Yan bindinga sun rugada sun harbe shi.

 

Koda karshe akayimasa tambaya akan cewa suna zargin wasu mutanan Dan Sarkin yace tabbas akwai wadan da suke zarginsu da hada baki da Yan bindingar domin kashe musu mahaifinnasu.

 

BA wannan bane Karan farko da Yan Bindiga suka saba kashen muta ne duk kuwa da wani Karan suna amsar kudin fansa sannan su kashe mutum .

 

Advertisement

Wannan ne yasa mutane basa iya bacci da idanu biyu rufe a wasu sassan Najeriya duk da kokarin da mahukunta ke yi na samun saukin matsalar.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending