Connect with us

News

Kamitin SCHSS ya wayar da kan mambobinsa da masu gudanar da DRF game da kundins da aka sabunta

Published

on

IMG 20240820 WA0014

DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA 

Domin tabbatar da dukkan masu ruwa da tsaki game da shirin samar da magunguna na saɓatta-juyatta (DRF) sun fahimci kundin ƙa’idojin shirin, Kwamitin Samar da Magunguna Mai Ɗorewa na Jiha (SHCSS) ya shirya bita ta kwana uku ga mambobin kwamitin da masu gudanar da shirin DRF a ƙanana da manyan asibitocin da suke gudanar da shirin.

Manufar bitar ita ce tabbatar da dukkan masu ruwa da tsaki sun fahimci lungu da saƙo na kundin domin tafiyar da shirin DRF yadda ya kamata a asibitoci.

Ƴan bindiga sun karbi kudin fansa sunƙi bayar da gawar Sarkin Gobir

Da yake jawabi, shugaban kwamitin kuma darakta mai kula da sashin magunguna ta ma’aikatar lafiya ta jihar Kano, Pharm. Kamilu Mudi Salisu ya ce wayar da kan masu ruwa da tsaki game da kundin ya zama wajibi, kuma ta zo a lokacin da ya dace, yana mai jaddada cewa bitar za ta sanar da su dukkan abubuwan da kundin ke dauke da su domin samun ingantuwar aiki a asibitoci.

 

Ya bayyana cewa za a sanar da mahalarta bitar dukkan abubuwan da kundin ke ɗauke da su, kalma bayan kalma, don su samu ilmin abubuwan da ya ƙunsa domin su rinƙa tuno yadda za su tafiyar da shirin a wuraren ayyukansu, ya tabbatar da cewa ta wannan hanya shirin DRF zai ci gaba da inganta a jihar Kano.

Advertisement

 

Cikin takaici ya yi nuni da cewa al’ada ce duk lokacin da aka sake nazarin irin wannan kundi aka rarraba, mafi yawan lokuta masu gudanar da shirin ajiye shi suke yi a ofisoshinsu, ba za su sake waiwayar sa ba sai lokacin da rikici ya taso sannan za koma masa domin samo mafita, inda ya yi fatan ɗabi’ar za ta canja a wannan karon.

 

“Mun san shirin DRF a jihar Kano ya jima, don haka ba za mu bar shi ya ruguje ba. Wasu daga cikin mu sun sha wuya matuƙa wajen ganin ɗorewar shirin. Zan iya bugar ƙirji na ce shirinmu na DRF shi ne mafi inganci fiye da yadda kuke tunani a faɗin wannan ƙasar.

 

“A matsayinmu na waɗanda shirinmu na DRF ya cimma nasara, ba za mu taɓa bari ya rushe ba. Wayar da kan masu ruwa da tsaki a kan wannan kundi da aka sake nazarta wajibi ne, kuma a lokacin da ya dace saboda za a sanar da mu dukkan ɓangarorinsa, ciki da bai, tare da fatan masu gudanar da shirin za su rinƙa bibiyar sa tare da aiwatar da abubuwan da ke ciki a kowane lokaci, ba sai matsala ta afku ba”, a cewar shugaban kwamitin.

Advertisement

 

Daga nan sai Pharm. Kamilu ya buƙaci mahalarta taron da su nutsu su mayar da hankali domin fahimtar maƙalolin da ƙwararru kan DRF, waɗanda ke da ilimi mai faɗi game da shirin tun lokacin da aka samar da shi.

 

Daga nan sai ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf saboda bayar da kulawa ta musamman ga sashin lafiya tun lokacin da ya hau karagar mulki, wanda hakan ya haifar da samun nasarori masu yawa cikin ƙanƙanin lokaci.

 

Haka kuma, ya jinjina wa ƙoƙarin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr. Abubakar Labaran Yusuf wajen tabbatar da sauya fasalin sashin ta hanyar bijiro da sabbin ayyuka da tsare-tsare, tare da sabunta waɗanda ya tarar domin haskaka tsarin.

Advertisement

 

Ya kuma jinjina wa shirin ‘Nutrition International’ da ke samun tallafin daga shirin ‘Forward in Action for Education, Poverty and Malnutrition (FAcE-PaM) don ɗaukar nauyin bitar, yana mai tabbatar musu da ƙudirin ma’aikatar lafiya ta jiha na ci gaba da aiki tare da su a kowane lokaci a shirye-shiryen irin wannan da suka shafi rayuwar al’umma.

 

Darktan Samar tare da Rarraba Magunguna na Hukumar Samar da Magunguna, Pharm. Tukur Ibrahim, Jam’in SCHSS na Hukumar kula da Manyan Asibitoci, Nura Yahaya da takwaransa na Hukumar kula da Ƙananan Asibitoci, Bello Muhammad Ɗandago, cikin ƙwarewa sun ilmintar da mahalarta bitar ɓangarori daban-daban na kundin, nasarori da ƙalubalen da shirin DRF ke fuskanta a asibitocin da ake tafiyar da shirin.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending