News
Trump Ya Sake Tsallake Rijiya Da Bayaa Wani Sabon Hari
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican Donald Trump ya sake tsallake rijiya da baya a wani sabon hari da wani dan bindiga ya yi yunkurin kai masa a filin wasansa na kwallon lambu a birnin Florida.
To sai dai kuma babu abinda ya samu Trump a wannan karon bayan jami’an hukumar FBI sun bayyana cewa sun dakile yunkurin kisan nasa.
Da yawa daga cikin jami’an sun yi ta harbi cikin daji ta inda aka ji motsi bayan ganin mutumin a dan tazara tsakaninsa da inda Trump ke wasa a cewar hukumomi.
Mutumin da ake zargi ya bar bindiga kirar AK-47 da kuma wasu kayayyaki bayan ya ranta a na kare cikin wata mota, sai dai daga bisani an cafke shi.
Wannan yunkurin kisan Trump na zuwa ne watanni biyu bayan an yi masa rauni a kunnen dama da bindiga yayin yakin neman zabe a Pennsylvania.
Wadannan lamuran da suka faru na nuna kalubalen da ke gaban jami’an tsaro na tabbatar da tsare rayukan ‘yan takara a zaben Amurka dake tafe cikin watan Nuwamban shekarar 2023.
DW
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
