News
Shugaba Tinubu Na Kan Haryar Zuwa Maiduguri Don Ganin Irin Ɓarnar Da Ambaliyar Ruwa Ta Yi
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Rahotanni na nuni da cewa shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, na kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri babban birnin jihar Borno, domin ganewa idonsa irin ɓarnar da ambaliyar ruwan da aka samu tayi wa birnin.
Idan dai ba a manta ba, a farkon makon da ya gabata ne aka samu ambaliyar ruwa a jihar, wacce ta shafe sama da kaso 70 a birnin Maiduguri, lamarin da ya hukumomi suka bayyana a matsayin annoba mafi muni da aka samu a birnin cikin gwamman shekaru.
Sa’aoi bayan faruwar lamarin ne dai mataimakin shugaban Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Sanata Kashim Shettima, ya isa birnin don jajantawa al’umma da gwamnatin jihar.
A cewar gwamnan jihar Babagana Umara Zulum, kimanin mutane miliyan biyu ne iftila’in ya shafa, inda daruruwan mutane suka bar gidajensu.
Tuni dai gwamnatoci da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma dai-daikun jama’a suke tashi tsaye wajen tallafawa waɗanda lamarin ya shafe, ganin yadda mutane ke cikin matukar buƙatar agajin gaggawa.
FRI
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
