Opinion
Banbancin Da Ke Tsakanin Muhammad Bello Matawalle Da Gwamna Dauda Lawal —Daga Imam Murtadha Gusau
Ya ku ‘yan uwana Zamfarawa, ya ku al’ummar arewa da al’ummar kasar mu mai albarka Najeriya baki daya, tabbas, duk mai bibiyar al’amurran da suke tafiya a kasar nan, wadanda suka shafi siyasa da matsalar tsaro, musamman yankin mu na arewa da kuma musamman yankin mu na jihar Zamfara, zai tabbatar da irin dauki-ba-dadi da cece-kuce da zazzafar adawa da zazzafar muhawarar siyasa da rashin shiri da rashin jituwa da ke gudana musamman tsakanin yaran mai girma Ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle da yaran mai girma Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare.
Allah ya sani, kuma shine shaida, kuma zamu mutu, zamu hadu a gabansa domin yayi muna hisabi, mu babu irin yunkuri da bamu yi ba domin ganin daidaito da sasantawa da shiri da fahimtar juna ya samu tsakanin wadannan bangarora guda biyu, domin samun zaman lafiya, kasancewar mun san irin alkhairin da ke tattare da samar da hadin kai tsakanin Ministan tsaro da Gwamnan jiha, game da sha’anin matsalar tsaron da yake damun jihar mu.
Jami’an Hukumar ICPC Sun Kama Kwaminshinan Kuɗi Na Zamanin El-rufa’i
Kasancewar jihar mu ta Zamfara tana cikin jihohin da suke gaba-gaba wurin fuskantar matsalar tsaro a Najeriya, shi yasa muke da fahimta da ra’ayin cewa, lallai da za’a samu cikakken hadin kai da fahimtar juna tsakanin wadannan shugabanni namu guda biyu, da tabbas, ko shakka babu za’a fi samun cikakkiyar nasara game da fada da ta’addanci da ‘yan ta’adda da suka addabi jihar Zamfara.
Ya ku jama’ah, ni zan yi bayani na gaskiya, kuma na tsakani da Allah akan wannan sha’ani. Kuma hakika na san wasu zasu yi maganganu akan abunda zan fada a yau. Amma wallahi ni ban damu ba, duk mai suka yayi tayi, duk mai zagi yayi tayi, duk wannan mun saba dauka, mun saba ji, kuma mun saba gani.
Tura ce ta kai bango shi yasa har na yanke shawarar yin wannan bayani.
Da ma kuma mu aikin mu shine bayyanawa al’ummah gaskiyar da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya bayyanar a gare mu; aikin mu shine, kokarin fitar da al’ummah daga cikin duhu game da abun da ya shige masu duhu. Kuma a duk lokacin da zamu yi bayani, wallahi bamu kallon mai yabo ko mai zagi. Bamu neman yardar kowa, face yardar Allah da amincewar sa. Bamu yiwa kowa fadanci ko banbadanci ko maula. Yardar Allah Subhanahu wa Ta’ala da amincewar sa kawai muke kallo kuma muke nema.
Duk wanda zai yi magana yayi, mu kawai abunda muke so shine, al’ummah su yanke hukunci. Kuma alhamdulillah, muna godiya ga Allah da ya hore muna dimbin al’ummah da suke fahimtar mu, kuma suka amince da mu, kuma suke da yakinin cewa ba zamu taba fada masu karya ba a duk abunda zamu fada masu ko zamu rubuta. Muna godiya ga Allah akan wannan.
A gaskiya tsakanina da Allah, game da wannan hayaniya da rikice-rikicen siyasa, da rashin jituwa, da rashin hadin kai wurin warware matsalolin da suke faruwa a jihar mu ta Zamfara, da rashin fahimtar juna da ke gudana tsakanin wadannan jagorori namu guda biyu, wato Gwamna Dauda da Minista Bello Matawalle, duk wanda zai tsaya da kyau, yayi adalci a cikin wannan lamari, wallahi zai fahimci cewa, Bello Matawalle shine yafi karkata da yarda da amincewa ga a samu shiri da hadin kai da fahimtar juna da zaman lafiya da hada karfi da karfe tsakanin shi da Gwamna Dauda.
Matawalle ya amince a zauna, Matawalle yace azo a hada kai ayi aiki tare. Matawalle yace azo a fuskanci jihar mu ta Zamfara. Amma duk wannan, babu abunda ake kokarin yi sai yunkurin watsa masa kasa a fuska. Sai kokarin dai sai an tozarta shi, sai an walakanta shi, sai an ci mutuncin sa. Babu abun da ake yi sai kokarin cin dunduniyarsa, sai kokarin bice wa tare da lullube duk wani kokari da yake yi, na ganin an cimma nasara.
Mun bibiyi dukkanin su biyu din, mun nemi jin ta bakin dukan su biyu din, mun yi yunkuri tare da kokarin hada wasu manyan ‘yan siyasar jihar mu ta Zamfara akan don Allah ayi hakuri, a manta da duk abunda ya wuce, a manta da banbancin siyasa, a tsaya a fuskanci wannan matsala ta tsaro da talauci, da suke addabar jihar mu. Amma tsakanina da Allah, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, mun samu cikakken hadin kai da goyon baya dari-bisa-dari daga bangaren Matawalle, amma daga bangaren Gwamna Dauda sam, bamu samu goyon baya ba.
Kai hasali ma, mutanen Gwamna Dauda, har kullun, idan kun nemi ganinsa, sai suyi banza da ku, su share ku, su manta da ku, kuma wai sai su rinka tsammanin wai kamar wani abu kuke nema a wurinsa, ko wani abu kuke so ya baku, ko kuma zuwa za ku yi wurinsa domin kuyi masa fadanci ko banbadanci, ko kuma ku kai wani kuka naku wanda ba na al’ummah ba.
Ya kamata mutanen Gwamna Dauda su bincika suji, ba yabon kai ba, ba kuma alfahari ba, kuma ba domin raini ga kowa ba, kuma ba wai mun fi karfin wani ya taimake mu ba, a’a, amma wallahi mu ba ma cikin masu bin ‘yan siyasa suna yi masu banbadanci da fadanci.
Tun da aka kirkiri jihar mu ta Zamfara mai albarka, Gwamnan ta na farko Jibril Bala Yakubu, muna Zamfara ya hau mulki har ya gama, har zuwa Gwamna na biyu, Ahmad Sani Yariman Bakura, har zuwa ga Mamuda Aliyu Shinkafi, har zuwa ga Abdul’aziz Yari Abubakar, har zuwa ga Muhammad Bello Matawalle, har zuwa ga shi Gwamna Dauda, da yake kan mulki a yau, idan akwai wanda muka nemi mu gan shi, ko kuma muka nemi wani abu a wurin shi, ko kuma muka yi masa wani banbadanci ko fadanci don Allah ya fadi ko ya bayyana.
Mu Allah ya sani, kuma shine shaida, ci gaban jihar mu da zaman lafiyar ta shine babban al’amarin da yake gaban mu. Kuma sannan muna da yakini da tabbacin cewa, hadin kan Gwamna Dauda Lawal, a matsayinsa na shugaban tsaro a jiharsa (Chief Security Officer), da Ministan tsaro, Muhammad Bello Matawalle, zai taimaki al’ummar jihar Zamfara baki daya. Hadin kan su, da sasancin su, da hada karfin da zasu yi, wallahi muna da fahimtar zai bayar da cikakkiyar natija, da izinin Allah, wurin kawo karshen wannan bala’i na rashin tsaro da yake addabar jihar mu.
Amma tsakanina da Allah, ina mai yi maku rantsuwa da Allah, mun samu cikakken hadin kai daga bangaren Bello Matawalle, amma daga bangaren Gwamna Dauda bamu samu wannan ba.
Ina mai fadar wannan ne tsakanina da Allah. Kuma ni kamar yadda kuka sani, ni ba dan siyasa bane, amma wallahi ina da wani abu guda, wanda yake shine, idan Allah ya fahimtar dani gaskiya, to ko shakka babu, tabbas, zan goyi bayanta kuma in karfafe ta, kuma in bayyana hakan, ba tare da kallo ko la’akari da duk abunda mutane zasu fada ba.
Allah shine shaida, tun muna magana da mutanen Matawalle, har ta kai ga mun yi magana da shi Matawallen kai tsaye, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, yayi muna rantsuwa da Allah, ya tabbatar muna da cewa, shi a shirye yake, ya bayar da duk wani irin goyon baya da ake bukata, domin samun tsaro a arewa da jihar Zamfara baki daya.
Matawalle ya saurare mu, kuma yana sauraron mu a koda yaushe. Kuma shi yasan ba wani abu yake bamu ba, kuma ba wani abu muke nema a wurinsa ba. Amma wallahi ya kira mu, mun kira shi, mun tattauna matsaloli tare, kuma ya nuna cewa shi al’ummarsa ce a gaban shi, kuma ya nuna shi mai sauraron al’ummah ne.
Amma daga bangaren Gwamna Dauda Lawal, kawai babu wani hadin kai, ko goyon baya, ko wani abu mai kama da haka da muka samu. Kai hasali ma, babu wanda zai saurare ku. Kuma sannan ga tsananin rashin yarda da kowa da suka yi, ga kuma tsammanin cewa kowa ma makwadaici ne, wani abu yake nema daga gare su.
To ya kamata su sani, a da can babu nemi komai a hannun wani Dan siyasar jihar Zamfara ba, balle yau ace za mu nema a hannun Gwamna Dauda. Kawai mu a matsayin mu na ‘ya ‘yan jihar Zamfara, masu kishin jiharsu, masu cike da bakin ciki tare da damuwa akan abunda yake faruwa a jihar, shi yasa muke ta kokari tare da yunkurin ganin cewa manyan mu su ji tsoron Allah, su hada kai, domin fuskantar wadannan dimbin fitintinu da suke addabar jihar mu.
Ba ma fadanci, ba ma banbadanci, ba ma neman komai a wurin kowa sai Allah Subhanahu wa Ta’ala, mai bai wa kowa da kowa.
Kuma ya kamata mu sani, su wadancan munafukai, masu cin abinci da rigimar siyasar da ke tsakanin Matawalle da Dauda, su sani, duk abunda suke yi Allah yana kallon su. Wadancan masu kokarin kange Gwamna Dauda daga jama’ah, wadanda basu son yayi sulhu da Matawalle, wadanda suke zuga wa, tare da ruruta wutar fada tsakanin Matawallen da Dauda, wallahi sai sun yi kunya. Da ikon Allah sai jihar mu taci gaba, sai ta samu zaman lafiya, in Allah yaso!
Kuma muna kira ga shi Gwamna Dauda, da kaji tsoron Allah. Kuma ka sani, ina mai yi maka rantsuwa da Allah, mai kowa mai komai, mamallakin komai da kowa, wanda babu abun bautawa da gaskiya sai shi, wanda zamu tashi a gabansa gobe kiyama, yayi muna hisabi, ka sani, wallahi, a irin bincike, da bin kwakkwafi da sauraro da muka yi, mun gano cewa Matawalle ba ya gaba da kai, Matawalle bai dauke ka makiyi ba, kamar yadda ake ta kokarin nuna maka a koda yaushe. Kuma Matawalle yayi muna rantsuwa da Allah da Alkur’ani, cewa shi al’ummah ce a gaban shi. Yayi muna rantsuwa da Allah da Alkur’ani cewa shi bai gaba da kai, bai kiyayya da kai, kuma shi a shirye yake da ku hada kai, ku hada hannu, kuyi aiki tare, kuyi abunda ya dace akan matsalar tsaron jihar Zamfara da ma arewa baki daya.
Ya kai Gwamna Dauda, ka sani, na san wannan sako nawa zai je gaban ka, kuma zaka karanta shi, to abunda muke fada maka shine, ka daina sausaron duk wani mutum, wanda yake nuna maka cewa Matawalle makiyin ka ne. Wallahi wannan sam ba gaskiya bane, kuma ba haka bane. Kawai suna amfani da wannan ne domin suci abinci.
Domin ni dai, a iya bincike da muka yi, mun tabbatar da cewa Bello Matawalle yana so kuyi aiki tare domin ceto jihar Zamfara daga matsalar da take ciki.
Kuma Gwamna Dauda kayi hakuri, wannan ita ce kawai hanyar da zamu aika maka da wannan sako. Kuma Allah ya sani, manufar mu ita ce bayyana maka, tare da bayyanawa al’ummar jihar Zamfara gaskiyar abun da yake faruwa. Kaji tsoron Allah, Ka yarda, ka amince, ku hada kai domin kuyi aiki tare, domin taimakon jihar mu mai albarka, musamman game da wannan matsala ta rashin tsaro da mummunan talaucin da suke addabar jihar mu.
Bamu ce dole sai kunyi siyasa iri daya ko jam’iyya iri daya ba, a’a, wannan ba shine manufar mu ba. Manufar mu ita ce, kowa yayi siyasarsa, amma ku hada kai domin ci gaban jihar mu. Ku zauna lafiya domin amfanin al’ummar mu. Manufar ku ta kasance daya, wato ci gaban jihar Zamfara da al’ummar ta kawai.
Mu sani, mulki na Allah ne. Yana iya bayar da shi ga duk wanda yaso, kuma yana iya kwace shi daga duk wanda yaso.
Bello Matawalle Allah ya kaddari ya zama Ministan tsaro, kai kuma Allah ya kaddari ka zama Gwamnan jiha, to me ya kamata kuyi, KU HADA HANNU DOMIN CETO JIHAR ZAMFARA, TARE DA KAWO MATA DUK WANI CI GABA DA YA DACE!
Gwamna Dauda, la’alla wannan rubutu ba zai yi maka dadi ba, kai da magoya bayan ka, amma ina kira da kuyi hakuri, wannan shine tsantsar gaskiya mai daci, wadda ban yi tsammanin na kusa da kai zasu iya fada maka ba. CEWA A GASKIYAR MAGANA, RASHIN JITUWAR DA KE TSAKANIN KA DA MATAWALLE, DAGA BANGAREN KA NE MATSALA TA KE!
Domin haka muna kira da ku gyara wannan matsala, domin ci gaban jihar mu mai albarka!
Kuma banbancin da yake tsakanin ka da Bello Matawalle shine, shi ya yarda kuyi aiki tare, kuma yana sauraron al’ummah. Amma kai a gaskiyar magana, babu wannan daga bangaren ka. Wannan shine banbancin!
Muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala Allah yasa ku gane hakan ku gyara, amin.
Daga karshe, muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala, mai kowa mai komai, mamallakin kowa da komai, ya kawo muna zaman lafiya da ci gaba mai dorewa, a jihar mu ta Zamfara, da yankin mu na arewa, da ma Najeriya baki daya. Wannan matsala ta rashin tsaro, da talauci, Allah ya yaye muna su, Allah yayi muna maganinsu. Wannan nasara da Allah yake ba wa jami’an tsaron mu akan ‘yan ta’adda, muna addu’a da rokon Allah Subhanahu wa Ta’ala yaci gaba da basu nasara. Allah ya mayar da dukkanin wadannan matsaloli namu su zama tarihi. Allah ya hada kan dukkanin manyan mu, domin su hada hannu su fuskanci wadannan matsaloli, amin.
Nagode, nagode, nagode.
Daga Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau. Za’a iya samun sa a lambar waya kamar haka: 08038289761.