Business
Warware Zare Da Abawa Tsakanin Kamfanin NNPCL Da Matatar Dangote A Kan Farashin Man Fetur
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Gwamnatin tarayya ko NNPC ba su suka kara farashin man fetur ba a wannan yanayi da ake ciki, kasuwa ce ke halin ta dangane da farashin man fetur
Haka zalika ba shi yiwuwa Matatar Dangote ta sai da man sa a faduwa, tunda farashin gangar mai ya zarce Dala 70 a kasuwar duniya.
A yanzu haka, a kan Naira 898 duk Lita Kamfanin NNPC Ltd ke sayan fetur daga matatar Dangwate. Akwai yarjejeniya tsakanin NNPC Ltd da Dangote inda zai rinka samar da Lita miliyan 25 duk Rana, Wanda zai fara daga ranar 15 ga watan Satumban 2024.
A ranar Asabar 14, ga watan Satumban 2024 Dangwate ya rubuto wasika cewa shi Lita Miliyan 16 kacal zai rinka samarwa. Sabanin Lita Miliyan 25 din da aka amince a yarjejeniyar. Ka ga za a samu gibin Lita Miliyan 8.2
Daga ranar da aka yi yarjejeniya cewa Matatar man Dangwate zata fara ba da fetur ranar 15 ga watan Satumban 2024 har ya zuwa17 ga watan Satumban, Lita Miliyan 5.8 kacal Dangwate ya samar. Wannan na nufin a cikin Lita Miliyan 50 da ya kamata Dangwate ya samar na kwanakin biyu, an sami gibin Lita Miliyan 44.2 wanda zai ba NNPC Ltd.
Bayan NNPC Ltd ya riga ya bayarda wasikar lamuni (wato Letter of Credit) na biyan Matatar Dangwate kudin Lita miliyan 25 duk Rana.
Tun daga bara kudin da ake sauke man fetur a Najeriya ya kai Naira 1,100. Amma NNPC Ltd ke cike gibin, don jama’ar Najeriya su rinka samun Mai akan Naira 620 duk Lita, kuma a rahusa.
Har Saida ta Kai NNPC Ltd ya fito ya baara, sakamakon gano cewa gibin fa da yake cikewa don jama’ar Najeriya su samu fetur cikin rahusa, ya yi yawa.
Ba gaskiya bane cewa Gwamnati ce ta kayyade yadda Dangwate zai saida Mai. Dangwate shi ne da kansa ya sa Farashin fetur dinsa yake saidawa NNPC Ltd akan Naira 898 duk Lita. Abi sananne cewa tun farko ma sama da naira 900 Dangwate ya so ya siyar da fetur dinsa duk Lita. Sai da NNPC Ltd ta sa baki sannan Dangwate ya dawo da shi Naira 898 duk Lita.
NNPC Ltd ya bukaci Dangote ya saidawa sauran dillalan man fetur in har suna bukata.
Babban dalilin da yasa NNPC Ltd ke sayen Mai wajen Dangote shine don tabbatarda Yan Najeria na sayen fetur a farashi Mai sauki.
Ba gaskiya sam sam batun cewa wai Dangwate ya so ya saida man fetur dinsa akan Naira 600 amma wai Gwamnati ce ta kara farashin. Tunfarko Dangwate ya so ya saida man fetur din sa ne akan kudi sama da Naira 900 amma NNPC Ltd ya dage sai ya sayar kasa da haka (wato Naira 898).