Connect with us

News

Yahaya Bello Bai Mika Wuya Ba  —Hukumar EFCC

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta bayyana cewa tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ba ya hannunsu tare da yin watsi ga duk wani rahoto da ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya mika wuya.

Advertisement

“Muna son sanar da cewa Yahaya Bello ba ya hannun mu. Mun bayyana nemansa ruwa a jallo a kan badakalar biliyan N80.2 kuma har yanzu babu abinda ya canja,” kamar yadda Dele Oyewale, shugaban sashen yada labarai na EFCC ya sanar a ranar Laraba.

Sauyin Yanayi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Barnar Da Ambaliyar Ruwa Tayi A Borno Da Zamfara A Taron Majalisar Kasashen Afrika

EFCC ta fitar da wannan sanarwa ne bayan kafafen yada labarai, ciki har da WikkiTimes Hausa, sun wallafa rahotannin cewa Yahaya Bello ya mika kansa ga hukumar a karon farko tunda ta fara nemansa a cikin watan Afrilu.

Advertisement

 

A cikin wani jawabi da Ohiare Michael, Darekta a ofishin yada na labarai na Yahaya Bello, ya fitar ya bayyana cewa toshon gwamnan ya amsa gayyatar EFCC a ranar bayan ya tattauna da iyalinsa da lauyoyinsa da abokan siyar sa.

Advertisement

Sai dai, a cikin sanarwar, Ohiare bai bayar da wani karin bayani a kan zuwan Yahaya Bello Ofishin EFCC ba kuma bai wallafa hotonsa a hedikwatar hukumar ba.

Ohiare ya kara fitar da wani jawabin inda ya kafe cewa Yahaya Bello ya ziyarci ofishin EFCC amma sabanin su yi masa tambayoyi a kan zargin da ake yi masa sai suka ce ya yi tafiyarsa.

Advertisement

Darektan ya kara da da cewa Yahaya Bello ya samu rakiyar gwamnan jihar Kogi mai ci, Usman Ododo.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending