Connect with us

News

Sauyin Yanayi: Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Barnar Da Ambaliyar Ruwa Tayi A Borno Da Zamfara A Taron Majalisar Kasashen Afrika

Published

on

IMG 20240918 WA0010
Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa, Benjamin Okezie Kalu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Gwamnatin Tarayya ta bukaci masu hannu da shuni a fadin duniya da su tallafawa kasashen Afrika da sauyin yanayi ya shafa.

Advertisement

Mataimakin shugaban majalisar wakilai ta kasa, Benjamin Okezie Kalu kuma shugaban tawagar Nijeriya a ci gaba da zaman majalisar wakilai daga kasashen Afrika dake gudana a kasar Afrika ta Kudu a ranar Talata inda ya bayyana matsayar kasar.

Ƴan Sanda Sun Kama Bindigogi 185, Harsasai 4,087, Da Ɓatagari 2,740

Da yake jawabi kan makalar da aka gabatar mai taken “Tasirin sauyin yanayi da tsarin Afrika na zuwa COP”, wanda daraktan shirye shirye da bincike na PACJA, Mista Charles Mwangi Nyambura ya gabatar, Kalu ya bada shawarar karbar haraji kan sauyin yanayi a kasashe masu rauni na Afrika.

Advertisement

Mataimakin shugaban majalisar, wanda ya koka kan ambaliyar ruwa da ta faru a jihar Borno da Zamfara ya ce shawarar harajin na sauyin yanayi zai taimaka wajen rage radadin da sauyin yanayi ya haifar a yankin.

Ya ce: ” Afrika ta tasirantu da illa na sauyin yanayi duk da cewa tana bada kashi 3.8 ga batun fitar da iskar idan aka kwatanta da kasar China dake fitar da kaso 23 da kasar Amurka mai fitar da kaso 19 da Turai mai kaso 13.

Advertisement

“Sauyin yanayi ya hana Afrika samun ci gaba da fimma muradin karni gami da walwalar mutane.

” A yau, kusan ‘yan Afrika Miliyan 600 basa samun wutar lantarki kamar yadda Bankin duniya ya fada”.

Advertisement

Jagoran na tawagar Nijeriya ya kuma bayyana illar da karancin abinci ke yi wanda sauyin yanayi ya haifar.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending