News
Ƴan Sanda Sun Kama Bindigogi 185, Harsasai 4,087, Da Ɓatagari 2,740
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ƴan sanda sun kama bindigogi 185, harsasai 4,087, ‘yan Boko Haram, ‘yan fashi da ‘yan bindiga da ɓatagari 2,740
Ashafa MurnaibyAshafa Murnai September 18, 2024
’Yan Sandan Kaduna sun kama mahara 36 a Kaduna, sun kwato shanu 486
Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana nasarar Taimako Mato, wani ƙasurgumin dillalin manya da ƙananan bindigogi da harsasai.
Sun kuma bayyana damƙe wani gogarman koyar da harbi da yadda ake sarrafa bindiga a wani sansanin Boko Haram.
An damƙe Mato tare da wasu ‘yan Boko Haram huɗu na gungun su.
Kakakin Yaɗa Labaran ‘yan sanda na ƙasa, Olumuyiwa Adejobi ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, a Abuja.
Ya ce a cikin watan Agusta ne jami’an tsaro suka samu wannan gagarimar nasara, a wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan.
“A farmaki daban-daban da jami’an ‘yan sanda suka kai wurare daban-daban kwanan nan, an samu gagarimar nasarar daƙile masu aikata manyan laifuka a wurare a faɗin ƙasar nan, ciki har da tarwatsa gungun masu safarar muggan makamai a yankin Bauchi da Filato.
“Cikin waɗanda aka kama akwai Taimako Mato, John Ɗanladi, Mohammed Munkail, Manasseh William da Muhammadu Haddi.
An same su da bindiga ƙirar PKT Mashinga ɗaya, jigidar albarusai 40. Shi shugaban na su, Taimako Mato, tantirin mai koyar da yadda ake sarrafa bindiga be a wani sansanin Boko Haram, kuma shi ne dillalan safarar muggan makamai ya na sayar masu.” Inji Adebutu.
Ya ce a wurare daban-daban kuma an samu nasarar kama ‘yan fashi da makami 295, masu garkuwa 271, kuma an kama harsasai 4087 duk a cikin watan Agusta.
Premium Times
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
