Connect with us

News

YAKI DA TA’ADDANCI: Ya Zama Wajibi Mu Kiyaye Harsunan mu, Mu Karfafi Jami’an Tsaron Mu, Muyi Masu Fatan Alkhair —Daga Imam Murtadha Gusau

Published

on

FB IMG 1726346637424

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai

Advertisement

‘Yan uwana ‘yan Najeriya! Tabbas daga cikin dukkan gabobin da suke cikin jikin Dan Adam, babu mafi saurin jefa mutum a cikin kogin halaka kamar harshen sa.

Harshe wata irin tsoka ce wadda babu kashi a cikinta. Amma kuma tana iya ruguza kowane irin kashi a cikin gangar jikin mutum gaba dayan sa!

Advertisement

Shugaba Tinubu ya saka hannu kan kudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba –NSA

Harshe ya kan iya warware imanin da ke cikin zuciyar Dan Adam! Harshe ya kan jawo wa gangar jiki bulala, ko jifa, ko kuma sara da kansakalin takobi. Harshe yana iya warware soyayya ko abokantaka ko dangantaka wadda ta dade. Harshe ya kan jawo fushin Allah a kan bawan sa. Harshe ya kan jawo wa mutum mummunan cikawa babu imani.

Harshe ya kan jawo a kifa mutum, a rika janshi a kan fuskarsa, a cikin wutar Jahannama.

Advertisement

Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Duk wanda ya kasance yayi imani da Allah da ranar lahira, to ya fadi alkhairi ko yayi shiru.”

Advertisement

Ya Allah ka bamu ikon fadar alkhairi da harsunan mu. Ka kiyayemu daga sharrin harsunan mu. Ya Allah ka bamu ikon fin karfin zukatan mu da harsunan mu, amin.

Ya ku al’ummar Najeriya! Tabbas, duk mai bibiyar al’amurra a kafafen yada labarai, da sauraron maganganun mutane, yana sane, yana ji, kuma yana ganin irin abun kunyar da wasu daga cikin ‘yan uwan mu ‘yan Najeriya suke aikatawa, na kokarin sare gwiwar jami’an tsaron mu, na kokarin sukar su da kuma aibata su.

Advertisement

Ko shakka babu, duk wani Dan kasa nagari, duk wani mutumin kirki, mai kishin kasar sa, wanda yake son kasar sa, yake nufin kasar sa da alkhairi, yake yi mata addu’a da fatan alkhairi, dole ka same shi yana tausaya wa bayin Allah, jami’an tsaron kasar nan. Dole ka same shi yana karfafa masu gwiwa, kuma yana yi masu addu’ar cin nasara, a duk wani yaki da suke yi da ‘yan ta’adda.

Jami’an tsaron nan fa mutane ne kamar mu. Suna da iyali, kuma suna da bukatu iri-iri, suna bukatar su rayu kamar kowa, amma duk da haka, suka shiga wannan aiki, suka amince su sadaukar da rayukansu, domin kasar mu Najeriya ta samu zaman lafiya, ta samu walwala da ci gaba mai dorewa.

Advertisement

Ya ku ‘yan uwana al’ummar Najeriya! Muna rokon ku, da ku dubi girman Allah, ku zamanto ‘yan kasa nagari, masu taya jami’an tsaron mu addu’ar samun nasara, tare da basu duk wani hadin kai da goyon baya da suke nema, wajen kawar da ta’addanci da ‘yan ta’adda, da duk masu tayar da zaune tsaye a kasar nan.

Ya zama wajibi a gare mu, mu karfafi jami’an tsaron mu, mu daina sare masu gwiwa, mu rinka yi masu addu’ar samun nasara, mu daina sukarsu da aibatasu!

Advertisement

Har kullun, ran duk wani mutumin kirki ya kan baci, ya kan ji babu dadi, idan yaji ko ya ga wasu lalatattun ‘yan Najeriya suna sukar jami’an tsaron mu.

Satin da ya wuce muna kan hanyar zuwa Gusau daga Kaduna, muka samu labarin cewa ga ‘yan ta’adda can sun tsare hanya, har sun kashe ‘yan sanda biyar da sojoji uku, akan wannan hanya ta Zariya zuwa Gusau, hanya mafi zama hadari a kasar nan.

Advertisement

Wannan hanya daga Zariya zuwa Gusau ta zama tarkon mutuwa. Babu ranar da ‘yan ta’adda basu tsare wannan hanya, su kashe na kashewa su sace na sacewa. Abun ya zama ruwan dare, kusan kullun sai sun tsare wannan hanya, su kashe kuma su dauki na dauka.

Hakika jami’an tsaron mu suna iyakar kokarin su, sun sadaukar da rayukan su, sun bar iyalan su, sun bar duk wani jin dadi, domin su ga Allah ya tabbatar muna da tsaro a kasar mu, amma wai duk da haka, sai ka ga wasun mu marasa kunya, marasa mutunci da kishin kasa da tsoron Allah suna sukar su, suna zagin su, suna aibata su, suna maganganun batanci da maganganun banza akan su.

Advertisement

A gaskiya ya zama dole kuma wajibi masu irin wannan mummunar dabi’a daga cikin mu suji tsoron Allah, su daina aikata irin wannan mummunan hali.

Kuma ya kamata mu sani, duk mutumin da kuka ga yana wannan to ba mutumin kirki bane, ba mai kishin kasar sa bane, ba dan kasa nagari ne ba, kuma babu alkhairi a tattare da shi.

Advertisement

Ta yaya za’a yi mutumin kirki ya zagi jami’an tsaron kasar sa? Ba zai yiwu ba. Duk wanda yake wannan mutumin banza ne!

Sannan ba mun ce wai basu yin laifi ko basu yin kuskure ba. Su mutane ne fa kamar kowa ne dan Adam. Suna iya yin daidai suna iya yin kuskure. To amma ba dalili bane, kuma babu wata hujja da mutum zai iya bamu, wadda zata iya gamsar da mu akan dalilin da zai sa shi yake batanci a gare su, da kuma abun da zai sa ba zai yiwa wadannan bayin Allah addu’ar samun nasara ba.

Advertisement

Don haka yaku ‘yan uwana ‘yan Najeriya, ku sani lokaci yayi da zamu sake tunani. Lokaci yayi da zamu bayar da dukkanin wani taimako da gudummawar da duk ta dace, ga jami’an tsaron kasar mu, game da wannan kalubale da suke fuskanta na yaki da bata-gari, ‘yan ta’adda.

Kar ka zama kai har kullun ba ka da aiki sai soke-soke. Kai kullun ba’a yi maka daidai ba. Idan jami’an tsaron mu sun ci nasara kayi bakin ciki, idan sun yi kuskure kafi kowa yada wa. Kana kwance a dakin matarka, wadannan bayin Allah suna fagen daga, amma baka da aiki sai mummunar magana a kan su.

Advertisement

Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Wanda duk yayi imani da Allah da ranar lahira, to ya fadi alkhairi ko yayi shiru.”

Advertisement

Idan ka san ba zaka fadi alkhairi akan jami’an tsaron mu ba, to kaji tsoron Allah kayi shiru, yafi maka alkhairi.

Kullun muna ta kuka akan matsalar rashin tsaro da ta addabe mu, amma wadanda suke fagen daga domin samar da tsaron nan, da duk wadanda suke iyakar kokarin su akan matsalar, ka kasance baka da aiki sai aibata su, sai zagi da cin mutuncin su. To ta yaya kake tsammanin za’a samu tsaron don Allah?

Advertisement

Shin baku san cewa miyagun maganganun mu suna iya yin mummunan tasiri wurin cin nasarar jami’an tsaron mu ba?

Ina cikin asibiti, kawai sai na ga an kawo wasu jami’an tsaro jina-jina, sun yi mummunan rauni, wasu ma sun rasa rayuwar su, duk dai saboda kishin kasar mu, amma duk da haka wasu suna ganin basu cancanci a yaba masu ba.

Advertisement

Haba ‘yan uwana ‘yan Najeriya! Ina kira a gare mu baki daya, don Allah masu irin akidar nan ta aibata jami’an tsaron mu, ya kamata su daina.

Allah yasa mu daina, amin.

Advertisement

Sannan game da manya daga cikin jami’an tsaron mu, su ma muna kira a garesu, da suji tsoron Allah, su tausayawa na kasa da su. Annabi Muhammad (SAW) yace:

“Duk wani babba da baya tausayawa na kasa da shi, da kuma karamin da baya girmama manya, to baya tare da mu.”

Advertisement

Don haka bai kamata ace manyan jami’an tsaron mu, ya zamo basa tausayawa na kasa da su ba.

Ya kamata manya daga cikin jami’an tsaro su daina tsorata ‘yan Najeriya, su daina hana matasan mu shiga aikin nan na tsaro, saboda irin munana mu’amala da yake faruwa tsakanin manya da kananan jami’an tsaro.

Advertisement

Abunda yake faruwa kwanan nan, na irin yadda ake musgunawa kananan jami’an tsaro, wallahi bai yi muna dadi, kuma abun bakin ciki da damuwa ne matuka.

Kafar nan ta kare hakkin bil adama da ke Birnin Abuja, mai suna Barkatai family, tana ruwaito wasu abubuwa da suke faruwa cikin wannan al’ummah na zalunci, cikin jami’an tsaro, wanda zai iya jawo muna fushin Allah Subhanahu wa Ta’ala a kasar nan

Advertisement

Firar da aka yi da Hussaina matar sojan nan, wanda aka tsare har tsawon shekaru shida, saboda kawai yaje sallah. Da firar da suka yi da Ramlat, ita ma matar wani soja, wanda ya bata a Fatakwal, wallahi abun tayar da hankali ne. Ina rantsuwa da Allah, da na kalli wadannan firar, sai da nayi kuka da hawaye. Hankali na ya tashi ba kadan ba.

Ya kamata manyan mu su sani, tsayar da adalci fa shine zai taimaka masu wurin cin nasara a cikin ayukkan su. Babu yadda za’a yi ya zamanto manya basu tausayawa na kasa, kuma ace suna son nasara a tare da su.

Advertisement

Don haka don Allah, don Allah, don Allah ya kamata mu gyara. Ya kamata dukkanin mu muji tsoron Allah cikin ayukkan mu. Mu sani, duk abunda muke yi Allah Subhanahu wa Ta’ala yana kallon mu. Kuma Allah ba zai bar zalunci ya tafi a banza ba!

Allah ya bamu ikon gyara wa bakin daya, amin.

Advertisement

Sannan daga karshe, ina kira ga dukkan ‘yan Najeriya da muyi hankali, muyi taka-tsantsan. Bai yiwuwa mu rinka daukar labarai wurin ‘yan ta’adda, ko wurin wasu makaryata. Yaushe har dan ta’adda ya zama mutumin kirkin da har zamu gaskata shirmen sa? Muyi hankali, ‘yan ta’addan nan suna kokarin wasa da hankulan mu. Suna so su gwara kawunan mu.

Wai sai kaga dan ta’adda yana kokarin bata sunan jami’an tsaron mu. Ko yana so ya bata sunan wani mutum daga cikin masu alaka da harkar tsaro, kuma a samu wasu jahilai daga cikin mu, suna kokarin yadda da abunda wancan kasurgumin dan ta’adda yake fadi. Don haka wallahi sai mun kiyaye sosai. Sam, Dan ta’adda ba abun amincewa ba ne, kuma su sam ba abun yarda ba ne.

Advertisement

Wassalamu alaikum,

 

Advertisement

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau ya rubuta. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending