Connect with us

News

Shugaba Tinubu ya saka hannu kan kudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba –NSA

Published

on

Tinubu ya saka hannu kan kudirin kafa cibiyar hana yaɗuwar ƙananan makamai ba bisa ƙa’ida ba – Ribaɗu

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa shugaban kasa Bola  Ahmad Tinubu ya rattaba hannu kan kudurin dokar kafa cibiyar kula da kananan makamai ta kasa.

Advertisement

Ribadu ya bayyana haka ne a wajen taron karawa juna sani kan hana yaduwar kananan makamai a Najeriya da kuma yankin yammacin Afirka a ranar Talata a Abuja.

Banbancin Da Ke Tsakanin Muhammad Bello Matawalle Da Gwamna Dauda Lawal —Daga Imam Murtadha Gusau

Ya ce hakan zai ƙara wa cibiyar kwarin guiwa wajen gudanar da ayyukanta.

Advertisement

A jawabinsa na bude taron, kodinetan hukumar NCCSALW na kasa DIG Johnson Kokumo mai ritaya, ya ce cibiyar a ‘yan kwanakin nan, ta samu wasu muhimman nasarori a yaki da yaduwar kananan makamai ba bisa ka’ida ba.

Kokumo ya ce, a ranar 1 ga watan Yuli, cibiyar ta kwato wasu tarin haramtattun makamai daga hukumar kwastam ta Najeriya, daga bisani kuma ta kama wasu mutane 10 da ake zargi da hannu wajen shigo da su ba bisa ka’ida ba.

Advertisement

Ya ce a halin yanzu hukumar NCCSALW tana tuhumar wadanda ake zargi da shigo da su Najeriya ba bisa ka’ida ba, da kayayyakin da aka haramta – Bindigogi 544 da harsasai 112,500 wanda ya sabawa sashe na 3 (6) na Dokar Laifukan Mabambantan Cap M17 na Tarayyar Najeriya 2004 da dai sauransu.

Cibiyar Yaki da Kananan Makamai ta Kasa (NCCSALW) ce ta shirya taron bitar.

Advertisement

Darakta Ibrahim Babani ne ya wakilci Ribaɗu a wurin taron.

 

Advertisement

 

Premium Times

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending