Connect with us

Business

Za A Haramta Sayar Da Motoci Masu Amfani Da Fetur A 2035

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta kulla kafa dokar da za ta haramta sayar da motoci masu amfani da man fetur ko dizel daga shekarar 2035.

 

Advertisement

Daftarin dokar ta wajabta haramta wa kamfanonin kera manya da kananan motoci yin masu fitar da hayaki gaba daya a 2035.

 

Advertisement

Mahaifin ɗan sandan da abokin aikinsa ‘ya kashe’ shi a Kebbi yana so a bi masa hakkinsa

Babban Mai Shiga Tsakani na Majalisar EU, Jan Huitema, ya ce, “Wannan albishir ne ga direbobi…sabbin motoci marasa hayaki za su kara yin sauki ta yadda kowa zai samu ya kuma mallaka.”

Advertisement

 

Shugaban shirin yaki da sauyin yanayi na EU, Frans Timmermans, ya ce, “Nahiyar Turai ta shirya komawa amfani da tsarin sufuri marar hayaki,” kuma yarjejeniyar sako ne ga masana’antar kera motoci da kwastomominsu.

Advertisement

 

Aminiya ta ruwaito cewa Dokar da Wakilai daga kasashen Tarayyar Turai 27 suka tsara za ta hana sayar da motocin da ke amfani da mai a fadin nahiyar.

Advertisement

 

Manufar dokar ita ce ganin an hanzarta komawa amfani da motoci masu amfani da wutar lanatarki da nufin rage sauyin yanayi.

Advertisement

 

Hukumar Tarayyar Turai da da Majalisar Tarayyar da wakilan kasashen sun sanya hannu kan yarjejeniyar a ranar Alhamis.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending