Connect with us

News

Jam’iyyar NNPP Ta Nemi  Amurka Da EU Da Kuma AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Jam’iyyar NNPP, ta nemi kasashen Amurka, Tarayyar Turai (EU) da Tarayyar Afirka (AU) su shiga tsakani kan shari’ar gwamnan Kano, inda ta danganta shari’ar a matsayin magudin hukuncin kotu domin kwace nasarar da Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya samu.

Leadership ta ruwaito cewa A zanga-zangar da aka gudanar a ranar Laraba a ofisoshin jakadancin Amurka, Tarayyar turai da tarayyar kasashen Afirka a Abuja, mukaddashin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ya ce, Kotun daukaka kara ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben jihar ta yanke, don haka, kotun ta nuna cewa, gwamna Yusuf ne ya lashe zaben da aka yi a ranar 18 ga watan Maris.

Advertisement

Mutane mu Suna Cikin Mawuyacin Hali -Kakakin majalisar wakilan Nijeriya

Ya kara da cewa, manufar zanga-zangar da jam’iyyar NNPP ta gudanar a ofisoshin jakadancin, ita ce ta sanar da dukkanin kasashe da kungiyoyi masu kishin Dimokuradiyy halin da kotunan zabe ke ciki a Nijeriya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending