Connect with us

News

Mutane mu Suna Cikin Mawuyacin Hali -Kakakin majalisar wakilan Nijeriya

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya ce ‘yan Najeriya na cikin mawuyacin hali, ya kuma yi kira da a mai da hankali kan kasafin kudin wajen jin dadin jama’a.

Advertisement

Abbas ya bayyana haka ne a ranar Laraba yayin gabatar da kudirin kasafin kudin 2024 da shugaba Bola Tinubu ya gabatar.

Zaben Kogi:Ba Zanyi Wahalar Zuwa Kotu Ba-Dino Melaye

Cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya yi da kuma hada kan farashin canji ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya.

Advertisement

Kakakin majalisar ya yi gargadin cewa bai kamata a kalli kasafin a matsayin “takardar kudi kawai ba.” Ya kara da cewa kasafin kudin dole ne ya yanke shawara don magance mafi mahimmancin bukatun ‘yan kasarmu da suka dade suna shan wahala.

 

Advertisement

Shugaban kasa, sanannen abu ne cewa miliyoyin al’ummarmu na rayuwa cikin mawuyacin hali. Don haka ne ma suke sa ran gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ta samar da mafita cikin gaggawa da kuma dorewa, inji Abbas.

Da yake magana kan bukatar shugaban kasa na amincewa da kasafin kudin kafin ranar 31 ga watan Disamba, Abbas ya ce kamata ya yi shugaban kasa ya tabbatar da MDAs sun bayyana a gaban kwamitocin domin sauraren korafinsu.

Advertisement

A wani labarin kuma Zaben Kogi:Ba Zanyi Wahalar Zuwa Kotu Ba-Dino Melaye

Najeriya da Angola sun ki amincewa da matakin da kungiyar kasashe masu arzikin fitar da man fetur ta duniya Opec ta bukaci su dauka, na rage yawan man da suke hakowa.

Advertisement

Rahotonni sun bayyana cewa, kawancen Kasashen da Saudiyya ke jagoranta ba su samu cimma matsaya ba da Angola da Najeriya, wadanda suka nuna rashin amincewarsu da rage yawan man da suke hakowa.

Wani wakili a yayin ganawar ya ce ba lallai ba ne a iya cimma matsaya a tsakanin bangarorin biyu kafin taron da kungiyar ta OPEC da za’a yi a gobe 30 ga Nuwambar 2023.

Advertisement

 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending