News
Gwamnatin Tarayya Zata Horas Da Mata Dubu Biyu Noman Zamani a Jihohi 6
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Gwamnatin Tarayya za ta horas da mata guda dubu 2, Da suka fito daga jihohin Jigawa da Adamawa da Kaduna sai nan Kano da jihar Anambra sai Neja da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja, harkokin da suka shafi noma a zamanance.
Ma’aikatar kula da walwalar mata, ta ce, an tsara shirin ne domin tallafa wa kungiyoyin hadin gwiwar mata da su shiga harkar noman shinkafa domin samun riba da dorewa, tare da hadin gwiwar wata kungiyar bunkasa aikin gona a nahiyar Afrika mai suna Green Agriculture West Africa Limited wadda ta kasance reshen kamfanin China na CGC.
Jam’iyyar NNPP Ta Nemi Amurka Da EU Da Kuma AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
Ana sa ran wannan mataki na gwaji zai karfafawa mata ta hanyar kafa kungiyoyin hadin gwiwa da kuma gudanar da ayyukan noma a zamance.
Ministar Matan ta bukaci samun hadin kai da goyon baya daga masu ruwa da tsaki na gwamnati da masu zaman kansu domin kara fadada tasirin shirin.
A wani labarin kuma Jam’iyyar NNPP Ta Nemi Amurka Da EU Da Kuma AU Su Kawo Mata Dauki Kan Zaben Gwamnan Kano
Ana ci gaba da musayar fursunoni tsakanin Isra’ila da Hamas a kwana na shida a jere bayan tsagaita wuta.
Ko wannan yarjejeniya zai ci gaba – wadda ba ta samu wata tangarɗa sosai ba – har gaba da wannan dare abu ne da babu tabbas a kansa.
Duka Hamas da Isra’ila sun nuna alamun tsawaita tsagaita wutar amma dai babu wata yarjejeniya da aka sanar zuwa yanzu, har ma jami’an Isra’ila na cewa suna ci gaba da shirin komawa fagen daga.
Benny Gantz, ɗaya daga cikin jami’an majalisar yaƙi ta Isra’ila, ya ce hakan zai iya faruwa a kowane lokaci kuma za su faɗaɗa hare-haren a faɗin Gaza.
A cewarsa babu wani gidan ɓuya. Wannan ya yi kama da gargaɗi ga mazauna unguwannin Khan Younis da Rafah da su fice daga gidajensu kafin ci gaba da yaƙin.
Gwamnatin Isra’ila ta bayar da umarnin gudanar da wani tsari, wanda da alama za a iya ci gaba da zaman lafiya har zuwa ƙarshen mako matuƙar dai Hamas za ta ci gaba da sako mutanen da ke hannunta.
Hakan zai bayar da damar sakin yara 100, da iyaye mata da kuma mata tsofaffi.
