Connect with us

News

‎Harkar Noma Na Fuskantar Kalubale A  Fadin Najeriya ‎

Published

on

A daidai lokacin da Najeriya ke fama da hauhawar farashin kayan abinci da tabarbarewar tattalin arziki, harkar noma – wacce ita ce jigon rayuwar miliyoyin ‘yan ƙasa – na fuskantar manyan matsaloli da ke barazana ga wadatar abinci da tsaron lafiyar jama’a.

‎Wasu daga cikin matsalolin da suka dabaibaye harkar noma sun haɗa da tsadar taki da iri, ƙarancin ruwan sama, rashin tallafin gwamnati, da kuma matsalar tsaro da ta hana manoma zuwa gonaki wasu yankunan.

Advertisement

Kotun Ƙoli Ta Tabbatar Da Sanata Monday Okpebholo A Matsayin Sahihin Gwamnan Edo.

‎A zantawa da wani babban manomi daga Ƙaramar hukumar Rogo dake jihar kano, ya bayyana cewa “Kafin wannan lokaci, buhun taki na urea ana siya NPK tsakanin N8,000 zuwa N10,000, amma yanzu ya kai fiye da 50,000. Wannan ya tilasta wa manoma rage yawan noma ko ma daina gaba ɗaya.”

‎Haka kuma, ana fama da ƙarancin kayan aikin gona na zamani da rashin samun bashi mai sauƙi daga bankuna ko gwamnati, lamarin da ke kara ƙara tsananta matsin lamba a kan talakawan manoma.

Advertisement

‎Bayan matsin tattalin arziki, matsalar tsaro ita ce babbar barazana ga noma a Najeriya. A jihohi da dama musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya, ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane sun hana manoma fita zuwa gonaki.

‎A jihar Benue, jihar da ke ɗaya daga cikin cibiyoyin noma a Najeriya, dubban manoma sun kaurace wa gonakinsu sakamakon rikicin makiyaya  da manoma da ke sanadiyyar Mutuwar mutane a ƙauyuka.

Advertisement

‎Wat  matsala da ba za a iya mantawa da ita ba ita ce sauyin yanayi. Gajeruwar damina da ambaliya sun lalata gonaki da dama a bara.

‎Rahotanni daga Jihohin Kebbi, Jigawa ,Borno, Yobe,da Kogi sun tabbatar da rushewar dubban hektoci na filayen noma sakamakon ambaliya.

Advertisement

‎Masana tattalin arziki da harkar abinci sun yi gargadin cewa idan ba a gaggauta ɗaukar matakan gyara ba, Najeriya na fuskantar barazanar karancin abinci a shekaru masu zuwa.

‎Gwamnati ya kamata ta mayar da hankali wajen ƙarfafa noma ta hanyar samar da rancen da bai da ruwa, rage haraji kan kayayyakin gona, da kuma tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin manoma.

Advertisement

‎Harkar noma ita ce ginshiƙin ci gaban kowace ƙasa. Idan Najeriya ta gaza farfaɗo da wannan fanni mai muhimmanci, hakan na iya jefa al’umma cikin yunwa da zaman dar-dar. Yanzu ne lokacin da ya kamata gwamnati da masu ruwa da tsaki su tashi tsaye don ceto wannan muhimmin bangare na tattalin arzikin ƙasa.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending