News
Kamfanin TCN Ya Tabbatar Da Lalata Babbar Layin Wutar Lantarki Mai Ƙarfin Kilo-volt 372-330kv.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) ya tabbatar da lalata babbar layin wutar mai rarraba wuta zuwa Damaturu a jihar Yobe da Maiduguri a jihar Borno.
Lamarin ya faru ne a kan titin Gombe – Damaturu-Maiduguri, inda aka lalata ginshikin wutar lantarki mai ƙarfin kilo-volt 372-330kv.
Ana Zargin Kusan Mutane 30, 000 Sun Kamu Da Cutar Farankama A Nahiyar Afrika A Bana – WHO
A wata sanarwa da Babban Manajan hulɗa da Jama’a na TCN, Ndidi Mbah, ya fitar a Damaturu, ya bayyana cewa waɗanda suka aikata wannan aika-aika sun yanke ƙafafu huɗu na ginshikin wutar, wanda hakan ya haifar da faɗowarsa sa.
Sanarwar ta bayyana cewa injiniyoyin TCN suna aiki domin samar da wuta ta wucin gadi zuwa Damaturu ta hanyar layin wutar lantarki mai ƙarfin kilo volt33 daga Potiskum. Maiduguri kuma za ta dogara ne da gidan samar da wuta na gaggawa har sai matsalar ta warware. Za a fara gyaran ginshikin da ya rushe nan take.
TCN ta yi Allah wadai da hare-haren da ake kai wa kan kayan wutar lantarki na ƙasa a kai a kai, kuma ta yi kira ga ‘yan ƙasa da su zama masu kula don samar da tsaro, tare da bayar da rahoton duk wani abin da ake zargi a wuraren da aka ajiye kayayyakin wutar zuwa ga jami’an tsaro ko ofisoshin TCN.
-
News7 days ago
Na Shiga Siyasa Ne Domin Yi Wa Al’umma Hidima —Tsohon IGP Suleiman Abba
-
News5 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News4 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
